Kocin Ingila, Thomas Tuchel, ya ce kalubalen da za su fuskanta daga Argentina da Lionel Messi zai fitar da mafi kyawun salon wasa daga wajen ‘yan wasansa.
Tsoffin abokan hamayyar za su yi karawa mai zafi a wasan kusa da na karshe na Gasar Cin Kofin Duniya ranar Laraba.
Wanda duk ya yi nasara a cikin su zai fafata da Spaniya a wasan karshe ranar Lahadi.
A cewar Tuchel, “Mun samu kura-kurai da yawa a wasanmu na baya, wanda ya hanamu yin tasiri mai kyau.
‘Mun yi gaggawa wajen yanke hukunci, ba mu da haƙuri kuma hakan ya shafe mu’ in ji shi.
- Super Falcons za su gwada karfi da Black Queens na Ghana a wasan sada zumunta
- AFCON 2027: Guinea ta buƙaci a sauya wurin wasanta da Afirka ta Kudu
“Mun samu ci gaba a gasar wajen kare gida a matsayin tawaga guda. Wannan shi ne abin da muka fi buƙata a wannan mataki akan Argentina”.`
“Mun kai wasan kusa da na karshe kuma muna da ƙishin nasara. Muna son samun nasara ta gaba. Wasa ne mai girma amma muna fatan yin shi kuma muna shirye.”
Don dakatar da Argentina, Ingila za ta bukaci ta dakile tasirin Lionel Messi. Dan wasan mai shekara 39 yana ci gaba da shanawa kuma yana cikin wanda suka fi kowa zira kwallo a gasar tare da kwallaye 8.
Tuchel ya ƙara da cewa, “Mun zo ne don mu buga wasan kusa da na karshe ta hanyar da muka tsara. Muna sane da girman kalubalen amma kuma mun shirya masa.”`