Lagos, 25 June 2025 African Championships

A shirye-shiryen ta na halartar Gasar Cin Kofin Mata ta Afirka karo na 14 wanda za a fara a Moroko ranar Lahadi, masu rike da kofin, Super Falcons ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunci da Ghana ranar Asabar a birnin Casablanca.

Falcons, wacce ta lashe gasar har sau 10, ta buɗe sansanin atisaye a Casablanca, babban birnin kasuwanci na Moroko, tun ranar Litinin, a shirinta na ƙarshe kafin wasansu na farko na Rukuni na C da Malawi a Rabat ranar Talata, 28 ga watan Yuli.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da Daraktan yada labarai na Hukumar Ƙwallon Kafa ta Najeriya, NFF, Ademola Olajire ya turawa gidan Rediyon Blueprint dake Abuja, ranar Talata.

A cewar sanarwar, izuwa yammacin Talata, ‘yan wasa 10 sun isa otal ɗin Super Falcons a Casablanca kuma ana sa ran ‘yar wasa Toni Payne, wacce kwanan nan ta koma kungiyar mata ta Inter Milan ta kasar Italiya daga Everton na Ingila, zata iso ranar Laraba.

A karkashin jagorancin Koci Justine Madugu, masu neman kare kofin sun halarci filin wasa na Stade el Arbi Zaouli a Casablanca ranar Talata domin atisayen su na farko.

‘Yan wasan da ke sansanin a yanzu sun hada da kyaftin Rasheedat Ajibade da masu tsaron raga; Chiamaka Nnadozie da Fatima Oloko da ‘yan wasan baya Oluwatosin Demehin da Glory Ogbonna da Christy Ucheibe da Shukurat Oladipo da Rofiat Imuran da ‘yar wasan tsakiya Jennifer Echegini da kuma ‘yar wasan gaba Asisat Oshoala.

Bayan wasan da Malawi ranar 28 ga Yuli, Falcons za su kuma buga da Zambia ranar Asabar, 1 ga Agusta da kuma Masar ranar Laraba, 5 ga Agusta a cikin Rukuni na C.

Dukkan ƙasashe 4 da za su kai wasan kusa da na karshe a Moroko za su samu tikitin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata na shekara mai zuwa a Brazil.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *