Takun-saƙa da kuma zafafan kalamai na ci gaba da karuwa tsakanin ‘yan wasannin tawagar kasar Spaniya da na Faransa, gabannin wasan kusa da na karshe na Gasar Cin Kofin Duniya da za su kara ranar Talata.
Da farko dai, Lamine Yamal na Barcelona ya gargadi ‘yan wasan Faransa cewa su “ji tsoron” Spaniya kafin wasan ranar Talata, inda maganarsa ta fusata wasu daga cikin manyan ‘yan wasan Les Bleus.
Ibrahima Konaté, mai tsaron bayan Faransa ya yi martani cewa, “Ba za mu ji tsoron kowa ba. Abu muhimmi shi ne mu ci gaba da tawali’un da muka fara gasar da shi, kuma mu guji faɗawa cikin irin waɗannan tarkuna, musamman a lokaci irin wannan.
- Mai tsaron gidan kungiyar Super Falcons ta bayyana shirin ƙungiyar gabanin gasar WAFCON
- “League Bloggers Awards” 2026: Ilechukwu da Nwobodo Sun kai Enugu Rangers ga nasara
- FIFA za ta ƙara yawan ƙasashe na Gasar Cin Kofin Duniya daga 48 zuwa 64 a shekarar 2030 – Infantino
“[Yamal] na iya faɗin abin da yake so. Za mu shirya don wasan ta hanya mafi kyau, kuma ina fatan bayan wasan sakamakon zai kasance a gare mu,” In ji konate.
Da aka tambaye shi yadda Faransa za ta iya dakile Yamal, sabon ɗan wasan Real Madrid din ya ƙara da cewa, “Spaniya ƙasace mai ban mamaki, da ‘yan wasa masu hazaka da yawa. Amma burinmu ba shi ne mu mai da hankali kan ɗan wasa ɗaya ba, saboda dukkan tawagar na iya cutar da ku. Ba Lamine kaɗai ba ne, dukkan Spaniya ce.”
Har wayau, Adrien Rabiot, ɗan wasan tsakiya, ya ce babu wani “Shiri na musamman don dakile Lamine Yamal” a wannan zagaye na sabon takun-saka tsakaninsu da ta fito fili tun a gasar Euro 2024.
“Idan aka yi la’akari da yadda muka buga wasanni har zuwa yanzu, mun isa wasan kusa da na karshe a cikin mafi kyawun yanayi. Karshen wasan ne kawai zai yanke hukunci, domin komai na iya faruwa a ƙwallo kafa.”