Gwarzuwar mai tsaron gidan ƙungiyar Super Falcons kuma mafi kyawun mai tsaron gida na mata a Afirka, Chiamaka Nnadozie, ta bayyana irin tsarin da Super Falcons ke shirin amfani da shi wajen kare kambun gasar da suke riƙe da shi, yayin da za a fara wasannin ƙarshe na gasar cin kofin matan Afirka (WAFCON) karo na 14 a ƙasar Maroko a wannan watan.

Nnadozie, wadda tana ɗaya daga cikin kwararrun masu tsaron gida na mata a duniya, kuma take kan shekara ta uku a jere a matsayin Gwarzuwar Mai Tsaron Gida ta Mata a Afirka, ta shaida wa shafin thenff.com cewa zakarun na kofin sau 10 suna shirin tunkarar gasar mataki-mataki (wasa-bayan-wasa) yayin da za su fafata a Rukunin C da kasashen Masar, Zambiya, da kuma sabuwar shiga Malawi, a gasar da aka tsara gudanarwa daga ranar 26 ga Yuli zuwa 16 ga Agusta a masarautar ta Arewacin Afirka.

“Za mu ɗauki wasannin daki-daki, wasa bayan wasa, domin ba za mu yarda mu yi tuntuɓe a kowane mataki saboda nuna wuce gona da iri na tabbacin nasara ba. Za mu mayar da hankali gaba ɗaya a kan burinmu guda biyu: samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya na FIFA da kuma kare kofinmu.”

“Abin sha’awa ne ganin yadda aka ƙara yawan ƙungiyoyi a wasannin ƙarshe (yanzu sun koma 16 daga 12). Wannan zai sa gasar ta kasance mai cike da zafi da gogayya, amma muna kwance kuma muna da natsuwa ba tare da la’akari da yawan ƙungiyoyin da ke wasannin ƙarshe ba.”

Haka zalika, mai tsaron gidan mai saukin kai ta ƙaryata ra’ayin cewa wasu rukunoni sun fi wasu ƙarfi a gasar ta mako uku da za ta gudanar da ƙasashe 16, inda za a buga dukkan wasannin a biranen Rabat da Casablanca.

“Ba na goyon bayan imanin cewa akwai wani rukuni da ya fi sauran wahala. Gaskiya ne, a yanzu haka a Afirka babu sauran ƙananan ƙungiyoyi. Za a sami abubuwan mamaki da yawa a wannan gasar domin wa waɗanda ake kira ƙananan ƙungiyoyi za su so su nuna cewa su ma ba na wasa ba ne, saboda haka dukkan ƙungiyoyi sun cancanci girmamawa kuma dole ne a dauke su da muhimmanci.”

“A gare mu, mun san abin da muke nema: Kofin gasar da kuma gurbin shiga gasar cin kofin duniya. Ba zai kasance da sauƙi ba, amma mu ne Super Falcons na Najeriya!”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *