Tsohon Sarkin Qatar Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani ne ya sauya ƙasar ta Yankin Gulf zuwa ɗaya daga cikin ƙasashe mafi arziki da tasiri a duniya. Ya rasu yana da shekaru 74.
Sheikh Hamad ya karɓi ragamar mulki ne a shekarar 1995, lokacin da ya yi wa mahaifinsa juyin mulki.
Ana ɗaukar shi a matsayin wanda ya za harsashin ginin kasar Qatar yadda za ta dace da zamani, inda ya jagoranci shirye shiryen ci gaba da sauye sauyen tsarin mulki da shirye shiryen ilimi ta hanyar amfani da dimbin arzikin gas da Allah Ya huwace wa kasar.
Sheikh Hamad ya hau mulki ne a 1995 lokacin da Qatar ta kasance ƙaramar ƙasa a Yankin Gulf.
Ta hanyar amfani da arzikin gas ɗin da take da shi, ya mayar da Qatar ɗaya daga cikin ƙasashe mafi arziki a duniya.
- Hurmuz zai ci gaba da kasancewa a bude duk da barazanar Iran – Trump
- Zan koma karatu bayan na yi ritaya daga ƙwallo — Osimhen
- Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin da ya hana INEC amincewa da taron majalisar jihohi na jam’iyyar ADC
A lokacin mulkinsa, Arzikin da kasar take samarwa (GDP) ya ƙaru fiye da sau 24, kuma a 2006 Qatar ta zama babbar kasa mai fitar da LNG a duniya.
Sheikh Hamad ya kafa Gidauniyar Qatar (wato Qatar Foundation), wadda ta jagoranci shirye shiryen ilimi da bincike.
Hakan ya kawo sauyi daga dogaro da man fetur zuwa gina tattalin arzikin da ya dogara da ilimi da fasaha.
A 1996, SheSauyi a Fannin Yada Labaraidan talabijin na Al Jazeera, tashar da ta tsinka takunkumin da ya yi wa kafafen yada labarai a yankin daurin huhun goro.
Tashar ta kuma zama murya mai ƙarfi musamman a lokacin Tunzurin Kasashen Larabawa (wato Arab Spring), lokacin da ta nuna zanga zangar neman tabatar da dimokuraɗiyya duk da haramcin da gwamnatoci suka yi mata a Masar da Siriya da Libiya.
Ya kaddamar da kundin tsarin mulki na dindindin na farko a 2004, tare da ba mata damar kada kuri’a da tsayawa takara.
Haka kuma, ya yi nasarar kawo Gasar Cin Kofin Duniya ta Kwallon Kafa Qatar a 2022.
wannan ya sa Qatar ta zama ta farko a tsakanin ƙasashen Larabawa da ta karɓi bakuncin gasar.
Sheikh Hamad ya sanya Qatar a matsayin mai shiga tsakani a rikice rikice ddaban-daban, kama daga Darfur zuwa Lebanon, har ma da tattaunawar Amurka da Taliban.
Amma abin da ya fi damun shi shi ne yakin ’yantar da Falasdinawa—ya ziyarci Gaza a matsayin shugaban ƙasa na farko cikin fiye da shekaru goma, inda sanya wa garuruwa a Gaza da Kudancin Lebanon sunansa.
Rasuwar Sheikh Hamad a shekara 74 ta kawo ƙarshen wani babi, amma hangen nesansa—kama daga sauyin tattalin arziki zuwa ga ’yancin kafafen yada labarai, daga sauye sauyen siyasa zuwa ga rawar da ya taka a ɓangaren diflomasiyya—ya tabbatar da cewa tasirinsa zai ci gaba da wanzuwa har bayan mutuwarsa.