Ɗan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen, ya bayyana cewa yana da burin komawa makaranta domin samun digirin jami’a bayan ya yi ritaya daga buga ƙwallon ƙafa.
A wata hira da ya yi da Instablog TV, wadda ke yawo a shafukan sada zumunta, ɗan wasan na Galatasaray ya ce duk da nasarorin da ya samu a harkar ƙwallon ƙafa, har yanzu ilimi na da muhimmanci a gare shi.
- ‘Yan Sandan Abuja sun gurfanar da mutum 3 gaban Kotu kan zargin kisan kai
- Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ƙarin kuɗin jarrabawar WAEC da NECO
- Sojoji sun daƙile harin ISWAP, sun gano ‘yan ƙasar waje dake taimaka musu
Osimhen ya ce rayuwa ta koya masa darussa da dama waɗanda bai koya a cikin aji ba.
Ɗan wasan mai shekaru 27 ya bayyana cewa rayuwar ɗan ƙwallon ƙafa ba ta da tsawo, don haka yana da muhimmanci a shirya rayuwa bayan yin ritaya.
Sai dai Osimhen bai bayyana lokacin da yake shirin komawa jami’a ba, ko kuma fannin da yake son karantawa.
