Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta gurfanar da wasu mutane uku a gaban Babbar Kotun Tarayya mai lamba 13 bisa zargin su da hannu a kisan Adimike Godwin, wanda ya kasance mahaifin mutum biyu daga cikin waɗanda ake tuhuma.

A cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar ‘Yan Sandan, SP Josephine Adeh, ta fitar, ta bayyana cewa waɗanda aka gurfanar sun haɗa da Adimike Odirachukwu Anthony da Adimike Chinyere Stephany da Comfort Ajibade.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 15 ga Mayun 2026 a unguwar Guzape da ke Abuja, bayan wani ɗan uwan mamacin ya sanar da ofishin ‘yan sanda cewa ba a iya samun Adimike Godwin ta waya kuma ba ya amsa kira.

Jami’an binciken ‘yan sanda sun isa gidan, inda suka tarar da shi kwance cikin ɗakinsa a sume tare da raunukan wuka da dama a jikinsa.

An garzaya da shi zuwa Asibitin Karu, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

A cewar sanarwar, jami’an bincike sun fara kama mutane biyar da ake zargi da hannu a lamarin.

Sun haɗa da mutanen uku da aka gurfanar da direban mamacin da kuma mai gadin gidansa.

Sai dai bayan kammala bincike, an gurfanar da mutum uku ne kawai a gaban kotu.

An gurfanar da su kan tuhume-tuhume guda huɗu da suka haɗa da haɗa baki domin aikata kisan kai da aikata kisan kai da kuma wasu laifuka ƙarƙashin Dokar Hana Auren Jinsi Ɗaya (Same Sex Marriage (Prohibition) Act).

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 30 ga Satumban 2026 tare da umartar a tsare mutanen ukun a Gidan Gyaran Hali na Suleja har zuwa ranar ci gaba da shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *