Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ce ta dakatar da shirin ta na ƙarin kuɗin rajistar jarrabawar WAEC da NECO na shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, Boriowo Folasade, ta fitar a ranar Litinin, ta ce ta janye ƙudirin nata har sai an kammala jin ra’ayin masu da ruwa da tsaki
Boriowo ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin ba da damar gudanar da cikakken nazari tare da tattaunawa da hukumomin shirya jarrabawar, da ma’aikatun ilimi na jihohi, da masu makarantu, da ƙungiyoyin iyaye, da na ƙwadago.
- Sojoji sun daƙile harin ISWAP, sun gano ‘yan ƙasar waje dake taimaka musu
- EFCC ta ɗaukaka ƙarar hukuncin diyyar Naira miliyan 10 a shari’ar Agunloye
- WAEC da NECO: Atiku yayi alawadai da ƙarin kuɗin jarrabawa
Sanarwar ta ce shirin ƙara kuɗin rajistar ya samo asali ne sakamakon hauhawar kuɗin gudanarwa, ciki har da tsaro, da sufuri, buga takardun jarrabawa, da amfani da fasaha da sauran ayyukan da ke tattare da ita.
Sai dai Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, ya bayar da umarnin dakatar da shirin domin tabbatar da cewa duk wata manufa da ta shafi ɗalibai da iyalansu ta kasance an sanya masu ruwa da tsaki.
Hukumar ta kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za ta ci gaba da sanar da jama’a duk wani mataki da za a ɗauka anan gaba.
A ranar 18 ga watan Yunin shekarar 2026 ne Ma’aikatar ta fidda sanarwar ƙarin, matakin da ya jawo cece-kuce da rashin jin daɗi daga ɓangaren iyayen yara da sauran Al’umma.