Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da ci al’umma. ƙara kuɗin jarrabawar kamala Babbar sakandare WAEC da NECO, yana mai bayyana sabon ƙarin a matsayin mataki mai tsauri ga al’umma.
Atiku ya ce wannan mataki ba ya la’akari da halin ƙuncin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke ciki, kuma ya saɓa wa nauyin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya ɗora wa gwamnati na tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar yin karatu.
A cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar yau Lahadi, Atiku ya ce abin takaici ne yadda a daidai lokacin da iyalai ke fama da hauhawar farashin kayayyaki, tsadar abinci, ƙarin kuɗin sufuri, tsadar wutar lantarki, ƙarancin kuɗaɗen shiga da rashin aikin yi, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta zaɓi ƙara tsadar ilimi
- Gwamnatin tarayya ta ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO
- Sojojin Bataliya ta 65 sun kama motar da ke ɗauke da manyan miyagun ƙwayoyi a hanyar Lagos zuwa Calabar
- Rushewar ginin Majalisar Dokokin Gombe: Mutum ɗaya ya mutu, bakwai sun jikkata
Ya jaddada cewa ilimi shi ne babbar hanyar da ke bai wa yara damar inganta rayuwarsu da kuma fita daga talauci, musamman waɗanda suka fito daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi.
Ya ƙara da cewa, duk da gwamnatin tarayya ta bullo da shirin Asusun Lamunin Ilimi ga ɗalibai (NELFUND), lamunin jami’a ba zai amfani yaron da aka riga aka hana ci gaba da karatun sakandare ba saboda tsadar.