Gwamnatin Tarayya ta amince da ƙarin  kuɗin rajista jarrabawar kammala babbar sakandare ta WAEC da NECO.

A yanzu dai za a biya naira 50,000 ga ɗaliban da za su rubuta jarabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO (SSCE), wanda zai fara aiki daga shekarar 2027.

Sabon kuɗin ya nuna ƙarin kusan kashi 82 cikin 100 idan aka kwatanta da kuɗin da ake biya a yanzu wanda ya kai naira 27,500.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Ilimin Sakandare na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Adeniji Ibrahim, ya sanya wa hannu.

A cewar sanarwar, wannan mataki ya biyo bayan taron da aka yi tsakanin hukumomin jarabawa da Ministan Ilimi a ranar 31 ga Maris, 2026, inda aka tattauna batun sake duba kuɗin jarabawa.

Ma’aikatar ta ce ministan ya umurci hukumar WAEC da NECO su yi amfani da kuɗi guda ɗaya wajen gudanar da jarabawar kammala sakandare.

Haka kuma, ma’aikatar ta umarci a sanar da dukkan masu ruwa da tsaki game da wannan sabon tsari.

Da take tabbatar da wannan batu a ranar Asabar, Daraktan yaɗa Labarai da hulɗa da Jama’a na ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta ce Gwamnatin Tarayya ta amince da ƙarin kuɗin jarabawar.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *