A ranar Juma’a ne Mai Shari’a C. Donglong na Babbar Kotun Jihar Plateau ya dage ci gaba da sauraron ƙarar da ake ƙalubalantar hukuncin ranar 9 ga watan Yuni, wanda ya ba wa Hausawan Karamar Hukumar Jos ta Arewa dake jihar haƙƙin zama ‘yan kasa, zuwa ranar 29 ga Oktoba, 2026.
Idan za a iya tunawa, a ranar 9 ga watan Yuni, 2026, Mai Shari’a Donglong ya yanke hukuncin cewa duk mutumin da aka bincika aka tarar Bahaushe ne kuma aka haife shi, ya kuma girma a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, to shi dan asalin yankin ne.
Masu shigar da ƙarar su biyu—Fatima Baba Akawu (mai ƙara ta daya) da mahaifinta Baba Alhaji Akawu (mai ƙara na biyu)—sun shigar da kara ne da Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa kan ƙin ba wa mai ƙara ta ɗ ɗ ɗaya takardar shaidan zama dan ƙasa.
Masu ƙarar sun tafi kotun ne domin ta fayyace batutuwa guda huɗu da suka haɗa da: Ko mai ƙara ta daya, bisa la’akari da cewa an haife ta ne a Jos ta Arewa kuma mahaifinta cikakken ɗan asalin yankin ne, tana da haƙƙin a amince da ita a matsayin ‘yar kasa kuma a ba ta takardar shaidar zama dan kasa, ba tare da la’akari da asalinta na kabilar Hausa ba.
Ko kin amincewa da bu ƙatar mai kara ta daya na neman takardar shaidar zama ɗan kasa da wanda ake ƙara ya yi, yayin da a lokaci guda kuma aka ba ta takardar shaidar zama mazaunin gari, sanka-ɗauka kuma aka ba wani mai suna Dung Bot na ƙabilar Berom takardar shaidar zama dan kasa a rana guda, ya ginu ne a kan nuna bambanci wanda ya saba wa doka a karkashin Sashe na 42(1), 42(2), 15(2) da (5), 17(1), (2)(a) da (3)(a) na Kundin Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (kamar yadda aka yi wa gyaran fuska) da kuma Shari’a ta 2 da ta 3 ta Yarjejeniyar Afirka kan Hakkin Dan Adam da na Al’ummu.
- An ceto ɗaliban Oyo bayan shafe watanni biyu a hannun masu garkuwa
- Tennis: Zverev ya kawo karshen burin Fery na buga wasan ƙarshe na Wimbledon 2026
- Sojoji, NEMA sun ƙara haɗin gwiwa domin tunkarar ambaliyar ruwa
Sai dai, yayin da aka zo sauraron ɗaukaka ƙarar da Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa ta yi kan hukuncin, alƙali mai shari’a ya dage ƙarar sannan ya tsaida rana domin yanke hukunci kan wani rukunin nuna rashin amincewa na farko (preliminary objection) da ke ƙalubalantar bayyanar wata sabuwar tawagar lauyoyi da ke wakiltar waɗanda ake karar, kafin a ci gaba da manyan aikace-aikacen da ke neman a soke hukuncin na baya.
A zaman na ranar Juma’a, lauyan Karamar Hukumar Jos ta Arewa, Garba Pwul (SAN), ya nuna rashin amincewarsa da bayyanar sabuwar tawagar lauyoyin da ke wakiltar waɗanda ake ƙarar, inda ya bayyana cewa lauyoyin ba su a cikin jerin sunayen farko na kotu kuma sun gaza bin dokokin kotu da suka shafi sauya lauya.