Al’amura su fara dawowa daidai a babban birnin Sudan, Khartoum, duk da cewa mazauna birnin na ci gaba da fargabar yiwuwar sake barkewar rikici.
Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutum miliyan biyu daga cikin mutane miliyan biyar da suka tsere daga gidajensu a Khartoum sun fara komawa gidajensu bayan nasarar da sojojin Sudan suka samu kan rundunar Rapid Support Forces (RSF).
Haka kuma, rayuwa na ci gaba da komawa a wasu garuruwa da dama bayan sojoji sun sake karɓe su daga hannun RSF.
- Ministocin tsaron kasashen AES na tattaunawa game da ayyukan rundunar hadin guiwa
- Kotun tsarin mulkin Senegal ta yi watsi da dokar da ke taƙaita ikon Shugaban Ƙasa
- Wata mata ta haifi jariri tana barci a kasar Canada
Sai dai tsakiyar birnin Khartoum, wanda a da ya kasance cibiyar kasuwanci mai cike da manyan shaguna da kamfanoni da unguwannin masu hannu da shuni, har yanzu ya zama tamkar kufai babu kowa. Wuraren da dama sun lalace, wasu kuma sun zama makabartu ko kuma wuraren da ake zargin an binne bama-bamai.
Matsalar wutar lantarki ta zama ruwan dare, yayin da ƙarancin ruwan sha ke ci gaba da addabar mazauna birnin.
Duk da irin mummunar lalacewar da ababen more rayuwa suka yi, mutanen da suka dawo sun bayyana farin cikinsu na sake ganin garinsu bayan shekaru da suka kwashe suna gudun hijira.
Sai dai alƙawarin da gwamnati ta yi na dawo da rayuwa cikin gaggawa bayan nasarar da sojoji suka samu bai cika ba.
Har yanzu ana fama da ƙarancin wutar lantarki, gine-gine da dama sun lalace, kuma ma’aikata da yawa ba su karɓi albashinsu ba.
Wasu daga cikin waɗanda suka dawo sun ce ba don sun ga dama ba ne, sai dai saboda matsin lambar da ake yi wa ‘yan gudun hijirar Sudan a ƙasar Masar.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa ƙasa da mutum 80,000 ne kawai suka koma tsakiyar birnin Khartoum ya zuwa yanzu.
An yi gumurzu daga titi zuwa titi tun lokacin da rundunar RSF ta ƙwace birnin a watan Afrilun shekarar 2023. Daga baya kuma, a bara, sojojin Sudan tare da ƙawayensu suka sake kwato yankunan bayan kazamin yaƙi.