Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa jami’an tsaro sun ceto ɗaliban makarantar Freedom da malamansu da aka sace a Jihar Oyo ba tare da biyan kuɗin fansa ba.
Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce yayin aikin ceto, jami’an tsaro sun kama mutane takwas da ake zargi da garkuwa da mutanen, kuma a yanzu suna hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS, domin ci gaba da bincike.
Onanuga ya ƙara da cewa gwamnati ba ta biya kuɗin fansa ko amincewa da musayar fursunoni ba domin tabbatar da sakin waɗanda aka sace.
Tsaro
- Yaran Borno da aka sace: ‘Ba mu san ko yaranmu suna raye ba’- Iyaye
- An sace dalibai sama da 600 a Najeriya a shekara uku
- ‘Yan ta’adda sun sace ɗaliban da ke rubuta jarabawar NECO a Borno
Ya kuma bayyana cewa ɗaya daga cikin jagororin masu garkuwar da suka buƙaci a sako yana ci gaba da fuskantar shari’a kan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.
An ceto ɗaliban da malamansu ne bayan sun shafe kusan watanni biyu a hannun masu garkuwa.