An yi garkuwa da akalla dalibai da malamai 603 a makarantu a Najeriya tsakanin watan Maris din 2024 zuwa Mayu 2026.
Masana sun dora alhakin yawaitar faruwar hakan kan rashin cikakken aiwatar da Tsarin Kare Makarantu wanda aka ware masa kudi Naira biliyan 145.
An kaddamar da Tsarin Kare Makarantun ne tun bayan sace daliban Chibok a 2014, inda masu ruwa da tsaki suka dora laifin kan rashin ingantaccen tsaro a makarantu da dama.
- Yajin aiki ya gurgunta koyo da koyarwa a Ibadan
-
A bamu Awanni “48” domin cafko Maharan Anambra -‘Yan Sanda
Wani bincike da jaridar Punch ta gudanar ya nuna cewa yayin wani hari da aka kai a ranar 7 ga Maris, 2024, a Makarantar Firamare da Sakandare ta LEA da ke Kuriga, Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, mahara dauke da bindigogi a kan babura sun sace yara ‘yan makaranta 137.
Bayan kwana biyu, a ranar 9 ga Maris, 2024, ‘yan bindiga sun kai hari a wata makarantar tsangaya a Gidan Bakuso, Karamar Hukumar Gada ta Jihar Sakkwato, inda suka sace dalibai 15, lamarin da ya kawo jimillar wadanda aka sace a farkon 2024 zuwa 152.
A ranar 17 ga Nuwamba, 2025, ‘yan bindiga sun sace dalibai mata 25 daga Makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta Maga da ke Karamar Hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi.
Bayan kwana hudu, a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, an kai hari Makarantar Katolika ta St. Mary da ke Papiri a Jihar Neja, inda aka sace dalibai 303 da malamai 12, ko da yake daga baya hukumomi sun ce an kubutar da su ta hanyar ayyukan hadin gwiwa.
A Jihar Kogi, a ranar 26 ga Afrilu, 2026, mahara dauke da makamai sun sace dalibai 23 daga makarantar marayu ta Daarul-Kitab da ke Zariagi, Lokoja, tare da matar mai makarantar.
A ranar 17 ga Mayu, 2026, an sace dalibai 42 bayan wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari wata makaranta a Mussa, Karamar Hukumar Askira-Uba ta jihar Borno.
A baya-bayannan, ranar 15 ga Mayu 2026, mahara dauke da makamai sun kai hari makarantu uku a Karamar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo, inda suka sace dalibai 39 da malamai bakwai, lamarin da ya kawo jimillar wadanda abin ya shafa zuwa 46.
Kungiyar Iyaye da Malamai da kuma Kungiyar Malamai ta Kasa sun koka cewa har yanzu makarantu da dama ba su da katanga da isassun jami’an tsaro, yayin da suka yi kira ga gwamnati da ta dauki matakin gaggawa don hana faruwar wasu hare-hare.
Shugaban Kungiyar Iyaye da Malamai ta Kasa, Haruna Danjuma, ya zargi gwamnatocin jihohi da yin watsi da nauyin da ke wuyansu na kare ilimi da tsaron yaran makaranta.
Sai dai gwamnatocin na jihohi kan kafa hujja da cewa ba su ne suke iko da hukumomin tsaro ba, don haka babu yadda suka iya.
Ko bayan sace yara da aka yi a Jihar Oyo, Gwamna Seyi Makinde ya ce babu yadda ya iya, sai ya zama Shugaban Kasa zai dauki mataki.