Jihar Bauchi ta sami tallafin kuɗi har na dalar Amurka miliyan 91.6 ($91.6 million) daga Bankin Zuba Jari da Bunƙasa Tattalin Arziki na ECOWAS (EBID).
Gwamnan jihar Bala Mohammed ne ya sanar da hakan da kan sa ga al’umar jihar cikin doki da farin ciki.
Bala Mohammed ya ce an bayar da tallafin ne domin samar da kuɗaɗen gudanar da manyan ayyukan hanyoyi da gadoji guda 24 a fadin jihar.
- WAFCON: Yadda Scorchers suka gasa wa Super Falcons aya a hannu
- Gasar WAFU B U20: Flying Eagles ta doke Black Satellites na Ghana da ci 4-2
- Tawagun maza da mata na Najeriya sun samu tikitin shiga Gasar Ƙwallon Kwando ta ƙasashen Afirka ta 2026
A cewarsa, wannan babban jarin zai inganta sadarwa tsakanin yankuna, ya ƙarfafa hanyoyin zirga-zirgar mu, ya sauƙaƙe tafiye-tafiyen mutane da jigilar kayan gona, ya faɗaɗa damar samun kasuwanni, sannan ya rura wutar haɓakar tattalin arziki a fadin Jihar Bauchi.
Sai gwamnan ya jinjina wa bankin EBID saboda amincewa da hangen nesan gwamnatinsa da ya yi.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar Jihar Bauchi cewa za a gudanar da waɗannan kuɗaɗe cikin gaskiya da riƙon amana da tsauraran matakan tattalin arziki domin tabbatar da an kammala kowane aiki cikin nasara.