Hukumar Tsara Jarabawar Larabci da Darussan Islama ta Kasa (NBAIS, ta ce kasafin kudin da ake warewa ma’aikatanta ya yi daidai da girman ayyukan da take gudanarwa, tana mai cewa ba daidai ba ne a ce hukumar ta cika da ma’aikata fiye da kima.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na hukumar, A.S. Ramalan, ya sanya wa hannu, NBAIS ta bayyana cewa daga cikin manyan ayyukanta akwai shirya jarabawar kammala makarantun sakandaren Larabci da Addinin Musulunci ga haɗaɗɗun makarantu a faɗin Najeriya, da kuma sa ido kan yadda ake koyar da darussan Larabci da na addinin Musulunci tare da sauran darussa na zamani.
Hukumar ta ce domin cika waɗannan nauyin da aka ɗora mata, ana ware mata kasafin ma’aikata a kowace shekara.
Ta ƙara da cewa sama da ma’aikata 2,000 daga cikin ma’aikatanta an tura su zuwa fiye da makarantu 1,000 a sassan ƙasar domin tabbatar da ingancin aiwatar da manhajar karatu da kuma kula da tsarin koyarwa.
Masana sun bukaci a soke Hukumar Tsara Jarrrabawar Larabci da Darussan Islama ta Kasa
Sanarwar ta kuma bayyana cewa kafin kafa Hukumar Kula da Almajirai da Yaran da Ba sa Zuwa Makaranta (NCAOSCE), NBAIS ce ke sa ido kan makarantun Tsangaya na Alƙur’ani.
Sai dai bayan kafa sabuwar hukumar, gwamnati ta amince da mayar da ma’aikata 2,000 daga NBAIS zuwa NCAOSCE domin ci gaba da gudanar da waɗannan ayyuka.
A cewar NBAIS, idan aka yi la’akari da faɗin ayyukanta da kuma yadda aka sauya wa wasu ma’aikata wurin aiki zuwa NCAOSCE, ba za a iya cewa hukumar ta yi wa kanta cunkoson ma’aikata ba kamar yadda wasu ke hasashe.
Hukumar ta kuma bayyana cewa Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (OHCSF) tare da tsarin IPPIS ne ke kula da kasafin albashin ma’aikatan ma’aikatu da hukumomin gwamnati, inda ake biyan albashi ta hanyar tsarin envelope wanda ke bai wa gwamnati cikakken iko kan biyan albashin ma’aikata.