Tawagar ‘yan wasan kwallon kafa ‘yan kasa da shekaru 20 ta Najeriya, Flying Eagles, na fatan samun tikitin shiga wasan kusa da na karshe da wuri a Gasar WAFU B U20 na bana wanda ke gudana a birnin Yamoussoukro na kasar Ivory Coast.
Flying Eagles za ta kece reni da tawagar Sparrow Hawks ta kasar Togo a wasansu na biyu a matakin rukuni a ranar Alhamis.
A wasan ta na farko da ta buga ranar Litinin, Flying Eagles wacce ke rike da kofin ta samu nasarar doke Black Satellites ta kasar Ghana da ci 4-2, inda ta kasance a matsayi na daya a rukunin B da bambancin kwallaye.
- WAFCON: Yadda Scorchers suka gasa wa Super Falcons aya a hannu
- Gasar WAFU B U20: Flying Eagles ta doke Black Satellites na Ghana da ci 4-2
- Tawagun maza da mata na Najeriya sun samu tikitin shiga Gasar Ƙwallon Kwando ta ƙasashen Afirka ta 2026
Ita kuwa Sparrow Hawks ta kasar Togo, ta sha duka ne a hannun tawagar Young Stallions ta kasar Burkina Faso da ci 3-0.
A na sa ran wannan fafatawa zai yi zafi sosai saboda dukkannin tawagun biyu, Flying Eagles da Sparrow Hawks na bukatar nasara a wasan.
A bangaren Flying Eagles kuwa, ta na neman nasara da wuri domin samun tikitin shiga wasan kusa da na karshe kafin karawar da za ta kasance mai zafi da Stallions na Burkina Faso a ranar lahadi.
Sparrow Hawks kuma za su yi iya kokarin su don samun sakamako da zai rayar da burinsu na ci gaba da kasancewa a gasar bayan matakin rukuni.
Nasara a ranar Alhamis, za ta bai wa Flying Eagles maki shida, tare kuma da karfafa gwiwar samun tikitin zuwa wasan kusa da na karshe don cimma burinsu na samun tikitin shiga gasar cin kofin Afirka na ‘yan kasa da shekaru 20 da za a buga a kasar Ghana shekara mai zuwa.