Ministan babban birnin tarayya (FCT), Barr. Ezenwo Nyesom Wike, ya bayyana cewa fara yakin neman zabe na ranar 19 ga watan Agusta gabannin babban zaben shekarar 2027 ba zai shafi ayyukan cigaba a babban birnin kasar ba. 

Ya ce Hukumar Gudanarwar FCT (FCTA) za ta yi amfani da ayyukan samar da ababen more rayuwa da ta gudanar a matsayin babban makamin yakin neman zabenta na shekarar 2027.

A cewar Ministan, “Yakin neman zabe yana nufin nuna abin da ka taba yi ne.

Wike ya ce  ba abin da za ka fada wa mutane idan ba ka da abin da zaka nuna musu.

Ya kara da cewa:”a  gare ni, yakin neman zabe yana nufin gabatar da sakamakon ayyukanka ne.

Ministan Babban Birnin Tarayyar ya ci gaba da cewa abin da kawai za mu yi shi ne mu koma ga mutane mu ce musu: ‘Mun yi muku wadannan kawayen, kuma mun cika su.’ Wannan gwamnati, muddin dai batun FCT ne, ta nuna sakamakon ayyukanta kuma ba za ta sami matsala wajen lashe zabe ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *