Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya ce tausayi ga Peter Obi da kuma halin da kasa ke ciki ne ya sa ya amince ya yia takarar Mataimakin Shugaban Kasa a zaben 2023.
Baba-Ahmed ya fadi haka ne yayin zantawa da kafar labarai ta Symfoni, wadda aka nuna a wani faifan bidiyo da ke yawo ranar Laraba.
A cewarsa, “Obi ya tunkari wasu manyan ‘yan siyasa guda uku a 2021, duk sun guje masa”.
“Da a ce a 2022 daya daga cikinsu ya tafi da Peter Obi da na yi murna. Amma duk sun guje mishi.
:Na ji tausayinsa. Na ji tausayin Najeriya a matsayin kasa…”, in ji Baba-Ahmed.
Baba-Ahmed, wanda ya fice daga jam’iyyar Labour zuwa jam’iyyar PRP a watan Mayu 2026, ya jaddada cewa goyon bayansa yana da iyaka kuma Obi ba shi da iko a kan makomar siyasarsa.
“Suna tunanin zan bi Peter Obi. Na nuna mishi isasshen tausayi a can baya. Cikin girmamawa, ba shi da iko a kan siyasata. Bai mallake ni ba, ni mai zaman kaina ne,” in ji Baba-Ahmed.
Idan ba a manta ba, a Zaben Shugaban Kasa na 2023 Yusuf Datti Baba-Ahmed ne ya yi takarar Mataimakin Shugaban Kasa a jam’iyyar Labour wadda ta zo ta uku.