Hukumar Zabe INEC ta sanar da sabon jadawalin fara kamfe da kuma zabukan shekarar 2027.
A karkashin sabon tsarin, jam’iyyun siyasa za su gudanar da zabukan fitar da gwani daga ranar 23 ga Afirilu zuwa 30 ga Mayu, 2026.
An tsayar da ranar 27 ga Yuni zuwa 11 ga Yuli, 2026 a matsayin lokacin mika shaidar tsayawa takarar Shugaban Kasa da na ‘Yan Majalisun Tarayya.
Ranar 18 ga Yuli zuwa 8 ga Agustan 2026 kuwa, shine lokaci da mabukata kujerar takarar Gwamna da na ‘yan Majalisun Jihohi zasu mika takardun tsayawa takara ta shafin intanet na hukumar.
Yakin neman zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya zai fara daga ranar 19 ga Agustan, 2026, kuma zai kare a ranar 14 ga Mutane/Zul-Hijja (14 ga Janairu, 2027).
A bangaren zaben Gwamnoni da Majalisar Jiha kuwa, za a bude damar kamfen ne a ranar 9 ga Satumbar 2026, sannan a rufe a ranar 4 ga Fabarairun 2027.
Hukumar ta INEC ta kuma tabbatar da cewa zata sake wallafa jerin sunayen yan takarar da aka amince da su a ranar 12 ga Satumbar 2026 daga matakin tarayya, sannan 10 ga Okutoba, 2026 ga yan majalisa a matakin jiha.
Ranar gudanar da zaben Shugaban Kasa da ‘Yan Majalisun Tarayya zai gudana ne a ranar Asabar, 16 ga Janairu, 2027.
Za’a gudanar da zabukan Gwamnoni da na ‘Yan Majalisar Jiha ranar 6 ga Fabarairun 2027.
INEC ta ce sabon jadawalin ya cika dukkanin sharuddan da Dokar Zabe ta 2026 ta tanada, wadda ta gindaya cewa lallai ne a fara yakin neman zabe kwanaki 150 kafin ranar zabe, sannan kuma a karkare sa’oi 24 kafin fara jefa kuri’a.