Rundunar Sojan Operation Fansan Yamma, sun dakile jerin hare-haren garkuwa da mutane a jihar Zamfara, inda suka ceto shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta Kauran Namoda, Dakta Aminu Yusuf, tare da wasu fararen hula.

Rundunar haɗin gwiwar ta ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar 28 ga Yuli, 2026, bayan da ta samu kiran gaggawa kan harin da ‘yan ta’adda suka kai a titin Tsohon-Tasha da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda.

Ta ce maharan sun kai hari gidan shugaban kwalejin, inda suka kashe jami’in tsaron sa, tare da raunata wani mutum guda, kafin su yi ƙoƙarin yin garkuwa da Dakta Aminu Yusuf da iyalansa.

 

Haka kuma a yankin Tungan Dorawa da ke Barkeji, sojojin sun dakile wani yunƙurin garkuwa da mutane, inda suka ceto fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Azaria, da wasu mutane 21 da aka sace.

Rundunar ta ce ta kama wani mutum mai suna Falalu Yusuf, mai shekaru 45, bisa zargin taimaka wa ‘yan ta’adda da bayanan sirri.

Operation Fansan Yamma ta ce za ta ci gaba da ƙarfafa ayyukan tsaro domin dawo da zaman lafiya a Zamfara da sauran sassan Arewa maso Yamma, tare da kira ga jama’a su ci gaba da bayar da bayanan da za su taimaka wajen dakile ayyukan masu aikata laifuka.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *