PRP Ta Bukaci Tinubu Da Ya Yi Murabus.

Jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) ta bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi murabus, tana mai zarginsa da gaza kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya yayin da matsalar tsaro ke kara ta’azzara a fadin kasar.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, inda ya ce

“A yanzu babu shakka cewa Shugaba Bola Tinubu ya gaza matuka wajen sauke babban nauyin da ya rataya a wuyansa na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya, Daga janarori zuwa kananan yara, babu wani dan Najeriya da yake cikin cikakken tsaro, Daliban makaranta sun zama cikin wadanda ake kai wa hare-hare, kuma bai kamata ‘yan Najeriya su dauki wannan a matsayin al’ada ba.”

Ya kuma ce bai kamata ‘yan Najeriya su jira zuwa zaben shekarar 2027 kafin su nuna rashin amincewarsu da yadda gwamnati ke tafiyar da harkokin tsaro ba, yana mai kira da a nemi daukar mataki cikin gaggawa.

Sai dai Fadar Shugaban Kasa ta sha nanata cewa gwamnatin Tinubu ta gaji matsalolin tsaro da suka dade suna addabar kasar, kuma tana ci gaba da amfani da jami’an tsaro da na leken asiri wajen yaki da ayyukan ta’addanci da sauran laifuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *