Gobara ta lalata shaguna a Jihar Oyo

Gobara ta tashi a wani layin shaguna da ke titin Balaro, yankin Oju-Odo Academy a Karamar Hukumar Ona-Ara ta Jihar Oyo, inda ta lalata shaguna takwas daga cikin guda 11 da ke wurin.

Mai bai wa Gwamna Seyi Makinde shawara kan gyaran harkokin kashe gobara kuma shugaban Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Moroof Akinwande, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:33 na safiyar ranar Laraba bayan samun kiran gaggawa.

A cewarsa, jami’an kashe gobara sun isa wurin cikin gaggawa tare da shawo kan gobarar kafin ta bazu zuwa sauran shaguna.

Akinwande ya ce har yanzu ba a gano musabbabin gobarar ba, kuma babu asarar rayuka ko jikkatawar kowa da aka samu sakamakon lamarin.

Ya kuma bukaci jama’a da masu shaguna su kasance masu lura da matakan kariya daga gobara, musamman ta hanyar samar da na’urorin kashe gobara a wuraren kasuwanci domin dakile aukuwar irin wannan matsala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *