Rundunar tace a bata nan da awanni 48 domin zakulo wadanda suka kai harin

Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Anambra, ta ce a  bata wa’adin awanni 48 domin cafke maharan da suka kaiwa ayarin motar Shugaban Ma’aikatan Gwamnan jihar Ben Nwankwo hari.

A wani taron gaggawa da aka gudanar a hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jiha da ke Awka, CP Orutugu ya bayyana harin a matsayin babban kalubale ga tsaron jihar.

Ya sanar da kaddamar da wani samame na musamman mai suna “Operation Fish Them Out”, tare da umartar jami’an tsaro su kara kaimi wajen tattara bayanan sirri da gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata harin.

Kwamishinan ya kuma gargadi matafiya masu amfani da hanyar Amansea-Ufuma da su kasance cikin shiri da taka-tsantsan, musamman a lokutan dare ya fara.

Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa rundunar ‘yan sanda na aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin kamo maharan, da kuma gurfanar da su a gaban kuliya, domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi al’umma.

Maharan sun yiwa ayarin motocin shugaban kwanton bauna a daren Lahadi, akan hanyar su zuwa yankin Amansea-Ufuma, mai iyaka da babban birnin jihar.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an ‘yan sanda biyu tare da jikkata wasu mutane, yayin da Ben Nwankwo ya tsira ba tare da wani rauni ba.

Hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a baya bayan nan na kara tsanan ta a jihohin Yammaci da Arewacin Najeriya, ko a ranar Litinin an kai hari tare da kwashe mutane a Jihar Kogi, yayin da gwamnati ke fuskantar matsin lamba game da kwashe dalibai a jihar Oyo makonni Uku da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *