Gwamnatin Tarayya ta umarci ma’aikatu da hukumomin gwamnati da su gaggauta daina bai wa ma’aikatanta abin da aka fi sani da hutun dole na watanni uku kafin su yi ritaya.
Umarnin na kunshe ne a wata takardar da Ofishin Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack, ta fitar tana cewa babu irin wannan tanadi a cikin dokoki da ka’idojin aikin gwamnati.
Takardar, wadda aka aike wa manyan jami’an gwamnati da suka hada da ministoci da manyan sakatarori, da shugabannin sassa da hafsoshin tsaro, ta bukaci jami’an da za su yi ritaya su bayar da sanarwar watanni uku.
“Abin da ake kira ‘hutun dole na watanni uku kafin ritaya’ ba shi da tushe a cikin dokokin aikin Gwamnati,” in ji Walson-Jack.
Shugabar Ma’aikatan ta jaddada cewa jami’an da ke shirin ritaya su ci gaba da zama ma’aikatan gwamnati a tsawon lokacin sanarwar, tare da gudanar da ayyukansu na yau da kullum, yayin da suke halartar tarukan bita da aka amince da su.
Ana sa ran wannan bayani zai shafi dubban ma’aikatan gwamnatin tarayya da ke gab da yin ritaya a kowace shekara.
Bisa ka’ida, ma’aikatan gwamnati suna yin ritaya idan sun kai shekaru 60 da haihuwa ko kuma bayan sun yi shekara 35 da fara aiki.
