A ranar Litinin, an rufe makarantun gwamnati a fadin jihar Oyo, biyo bayan yajin aikin da Malamai suka shiga sakamakon rashin tsaro.
A makon da ya gabata ne kungiyar malamai (NUT) ta umarciĀ dukkanin Malaman jihar su tsunduma yajin aiki, a bisa dalilan tsaro da suka kai ga sace dalibai da malamansu, da kuma cigaba da garkuwa da su.
Rahotanni daga Jihar ta Oyo na cewa makarantu sun kasance a garkame a birnin Badin, kuma ana iya hango gungun malamai tsaye a bakin kofofin shiga.
An kuma gano cewa yajin aikin ya shafi dalibai da ke rubuta jarabawar kammala sakandare (WAEC), inda jami’ai dake kula da rubuta jarabawar suka yi cirko-cirko a kofofin shiga makarantun.
Kwanaki kadan da sace daliban ne Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da a dauki jami’ai dake kare gandun daji guda dubu daya, tare da kuma aika runduna ta musamman domin ceto wadanda akayi garkuwar dasu a jihar ta Oyo.
Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanuga ne ke bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Onanuga ya ce Tinubu ya dauki wannan mataki ne biyo bayan ziyarar da wata tawagar gwamnatin tarayya ta kai Unguwannin Esiele da Yawota, a yankin karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo.
Rahotanni daga Birnin na Badin na nuni da cewa mazauna birnin sun gudanar da wata zanga-zangar matsawa gwamnatin Seyi Makinde lambar a gaggauta dawo musu da wadanda aka yi garkuwa dasu, ganin yadda lokaci ke kara tsayi

Kawo yanzu, babu wani rahoto da ya shafi nasarar da aka samu wajen dawo da daliban da malaman su da aka sace, illa zaman dar-dar a zukatan mazauna birnin dake tattauna lamarin a matsayin labari mafi daukar hankali.