Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Dan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa a Jam’iyyar NDC Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi watsi da jita-jitar da ke yawo a kafafen sadarwa.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na Facebook, Kwankwaso yace babu gaskiya a sakon da ake yadawa wacce ke ikirarin cewa yana shirin shirya zanga-zanga kan kalubalen tsaro da ke fuskantar kasar nan.
“Hankalin mu ya karkata zuwa ga wani sako da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani a halin yanzu, wanda ke ikirarin karya cewa muna shirin gudanar da zanga-zanga kan karuwar rashin tsaro a kasar nan”-
“Ba ma goyon bayan kowane irin mataki da zai iya kaiwa ga rugujewar doka da oda, ko kuma asarar rayuka da dukiyoyin al’umma,” in ji sanarwar” Inji Kwankwaso
Kwankwaso ya jaddada cewa a matsayinsu na shugabanni, sun yi amanna da hanyoyin lumana da tattaunawa wajen magance matsalolin kasa, maimakon tayar da hankalin jama’a.
Ya kara da cewa tsarin dimokuradiyya ya samar da ingantacciyar hanyar da mutane za su nuna ra’ayinsu ko neman canji, wato hanyar zabe, wadda itace sahihiyar hanya mafi inganci ta nuna rashin gamsuwa ko neman sauyi a gwamnati.
Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyarsu ta NDC tana da cikakken kwarin gwiwar samun gagarumar nasara a zabuka masu zuwa ta hanyoyin lumana na dimokuradiyya.
A karshe ya yi kira ga al’umma da su guji amfani da bayanai marasa tushe, sannan su yi watsi da duk wata jita-jita ake kokarin yadawa domin haifar da rudani.
