Kungiyar kare hakkin ‘Dan Adam ta Amnesty International tayi Allah-wadai da rushe wani bangare na Unguwar Durumi a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce motocin rusau mallakar hukumar babban birnin tarayya ne suka shiga Unguwar ta Durumi da misalin karfe Bakwai na safiyar ranar lahadi suka fara rusa gidaje yayin da mutane ke zaune a ciki.
Amnesty ta ce hakan ya sabawa dokokin kare hakkin Dan-Adam na duniya, inda ta zargi gwamnati da nuna halin ko’in kula da take nunawa akan matsalar muhalli da alumma ke ciki.
Wani mazaunin yankin na Durumi mai suna Thomas da aka rushewa shago, ya bayyana rashin jin dadin wannan mataki da Hukumar Babban Birnin Tarayyar ta dauka, da yace ya haifar masa tafka asarar dukiya mai yawa.
A baya bayan nan hukumar tsara birane ta birnin Abuja ta tsananta rushe matsugunai da ta kira da wurare masu hadari dauka akan su.
Cikin wata sanarwa da Mai Taimakawa Ministan Abuja a bangaren yada labarai Lere Olayinka ya fitar a ranar Juma’a 29 ga watan Mayu, ya ce hukumar na duba yiwuwar kwace lasisin wasu Otal-Oatal da wuraren shakatawa, dake zamewa mazauna birnin barazanar tsaro.
