Abdul Samad Isiyaku Rabiu ya yi nasrar darewa matsayin mutum na biyu mafi wadata a Afirka a bana

A farkon wannan watan ne kafar yada labarai ta Bloomberg ta ayyana Abdul Samad Isiyaku Rabiu a matsayin mutum na biyu mafi wadata a nahiyar Afirka.

Wannan bayani dai ya zo da ban mamaki, cewa ya sha gaban Johann Rupert na Afirka ta Kudu –  yanzu shi ne yake biye da Aliko Dangote.

Hakan na nufin mutum biyu da suka fi kowa wadata a Afirka ’yan Najeriya ne kuma ma Kanawa.

Ko da yake a yau sunan Abdul Samad ya shiga cikin sunayen manyan masu arzikin duniya, labarinsa ba da biliyoyin daloli ya far aba – daga ƙananan matakai fara a birnin Kano.

A farkon wannan shekara ta 2026 dukiyar Abdul Samad, wanda shi ne ya kafa kuma yake shugabantar Rukunin Kamfanonin BUA (wani lokaci akan yi mishi lakabi da BUA), ta haura zuwa kusan dala biliyan 19.

Ta yi wannan hauhawa da ta kai ta kusan dala biliyan 9 a ne kuma a cikin ’yan watanni kaɗan.

Makasudin hakan kuma shi ne nasarar manyan kamfanoninsa guda biyu, BUA Foods Plc da BUA Cement Plc, wadanda dukkansu suke kasuwar hannayen jari ta Najeriya.

Arziki a Masana’antu

Tun a 1988 Abdul Samad ya fara harkar kasuwanci ta hanyar shigo da ƙarafa da sinadarai, amma daga baya ya faɗaɗa zuwa yin siminti da sukari da kuma harkar gidaje.

Babban matakin da ya ɗauka — na haɗe kamfanin Obu Cement da Kamfanin Siminti na Arewacin Najeriya (CCNN) a 2020 — ya tabbatar da BUA Cement a matsayin kamfani na biyu mafi girma wajen samar da siminti a Najeriya.

A yau, Abdul Samad ne ya mallaki kashi 98.2 cikin 100 na hannun jarin BUA Cement, wanda ya zama sanadin samun dukiya mai yawa a gare shi yayin da buƙatar kayan gini ke ƙaruwa a Yammacin Afirka.

A gefe guda kuma, kamfanin BUA Foods, wanda Abdul Samad ya mallaki kashi 95 cikin 100 na hannun jarinsa, ya zama ginshiƙi a kasuwar kayayyakin abinci ta Najeriya, inda yake samar da sukari da taliya da shinkafa da mai.

Duk da matsalolin hauhawar farashin kaya, kayan kamfanin sun ci gaba da yin kasuwa, lamarin da ya haifar da ƙaruwa a kimar hannayen jarinsa, ya ƙara ɗaga darajar Abdul Samad.

Yau da Gobe

Ba ƙwarewar kasuwanci kawai cigaban Abdul Samad ya nuna ba, har ma da ƙarfin masana’antun Najeriya.

Duk da cewa har yanzu kamfanin Siminti na Dangote ne jagora, kamfanonin Abdul Samad sun yi tasiri sosai, sun kuma sa ya zama babban abokin gogayya a fagen tattalin arzikin kasar nan.

An kiyasta dukiyar Dangote ta kai dala biliyan 34.4, yayin da a yanzu Abdul Samad ya sha gaban Johann Rupert mai dala biliyan 17.7.

Yayin da Abdul Samad yake ƙarfafa matsayinsa a tsakanin manyan masu arzikin Afirka, ana ci gaba da yin tambayoyi game da yadda matsalolin tattalin arzikin Najeriya — daga faduwar darajar kuɗi zuwa hauhawar farashin kaya — za su iya shafar daularsa.

Amma a halin yanzu, yadda darajarsa ta yi tashi mai ban mamaki shaida ce ta tasirim haɗa kamfanoni da kuma buƙatar kayayyakin abinci da gini da ba su taɓa gushewa ba.

Wane ne Abdul Samad?

An haifi Abdul Samad Isiyaku Rabiu ne a Kano a shekarar 1960.

Mahaifinsa, Khalifah Isiaku Rabiu, shahararren ɗan kasuwa ne a Arewacin Najeriya.

Wannan ya say a samu da horo tun da wuri, inda ya koyi kasuwanci daga gida kafin ya tafi karatu a Amurka.

A 1988, Abdul Samad ya kafa Rukunin Kamfanonin BUA, da farko yana shigo da ƙarfe da sinadarai.

Amma bai tsaya a nan ba — ya ga damar faɗaɗa harkokinsa zuwa masana’antun siminti da sukari da abinci ya kuma yi amfani da ita.

Wannan hangen nesa ya sa ya zama ɗaya daga cikin manyan masu masana’antu a Najeriya.

Hangen Nesa da Nasara

Abdul Samad ya yi fice wajen haɗe kamfanoni daban-daban wuri guda da faɗaɗa kasuwanci.

Haɗe kamfanin siminti na Obu Cement da kamfanin CCNN ya tabbatar da shi a matsayin babban mai samar da siminti.

A gefe guda, kamfanin BUA Foods ya zama ginshiƙi a kasuwar abinci ta Najeriya, yana samar da kayayyakin da ake buƙata kullum.

A farkon 2026, dukiyarsa ta karu, ta kai kusan Dala biliyan 19, lamarin da ya sa ya zama mutum na biyu mafi arziki a Afirka, bayan Aliko Dangote.

Wannan ya nuna yadda hangen nesa da juriya ke iya sauya rayuwa daga matakin kasa zuwa matakin duniya.

Bayar da Gudummawa

Baya ga kasuwanci, Abdul Samad ya kafa Cibiyar Afirka ta Abdul Samad Rabiu (ASR Africa), wadda take bayar da tallafi a bangaren kiwon lafiya da ilimi da da ci gaban al’umma.

Wannan ya nuna cewa nasararsa ba ta tsaya ga tara dukiya ba, har ma da bayar da gudummawa ga al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *