Rundunar 'Yan sandan tace dole ne ta dauki matakin domin kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar Kano

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta bayar da umarnin soke gagarumin Hawan Daushe da aka shirya gudanarwa a jihar, domin tabbatar da tsaro.

A  wata wasiƙa da Blueprint Radio ta gane wa idanunta, wadda ta fito daga ofishin Mataimakin Kwamishinan ‘Ƴan sanda na Jihar, DCP Lawal Isa Mani,Rundunar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin daƙile duk wata barazana ga zaman lafiyar al’umma.

Yadda lamarin ya fara
Tun da farko, Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya aika da wasiƙar neman izini zuwa ofishin Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar a ranar 17 ga watan Mayu, inda ya bayyana aniyarsa ta gudanar da Hawan Sallah a bana.
Sai dai, a ranar Alhamis 28 ga watan Mayu, Rundunar ta haramta wa Sarki Aminu Ado Bayero gudanar da hawan domin kauce wa barkewar tashin hankali.

Martanin Ɓangaren Sarki Aminu
Da yake magana a madadin ɓangaren Sarki Aminu Ado Bayero, Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Ɗan-Agundi, ya tabbatar da cewa sun sami umarnin ‘yan sandan kuma sun dakatar da dukkan shirye-shiryen da suka yi na hawan.

“Mun karɓi wannan shawara (ta ‘yan sanda) a matsayin wata jarrabawa ko ibtila’i da ya shafi ɓangarorin masarautar Kano baki ɗaya cikin shekaru biyu da suka gabata,” in ji Alhaji Aminu Babba.

Majalisar Sarki Sanusi II
A gefe guda kuma, Fadar Sarki Muhammadu Sanusi II (Sarki na 16) ma ta sanar da soke nata shirye-shiryen na gudanar da hawan sallar.
A wata sanarwa da ya fitar, Matawallen Kano Alhaji Aliyu Ibrahim ya ce Majalisar Masarautar ta sami bayanan sirri game da yunkurin wasu na tayar da husuma da ka iya kaiwa ga asarar rayuka.
Matawallen ya ƙara da cewa: “Bayanai da muka samu sun nuna cewa wasu gungun mutane na ƙoƙarin shigo da ‘yan ta-adda Jihar Kano domin su tayar da hargitsi a lokacin bukukuwan Babbar Sallah.”

Saboda haka, a cewar Matawallen, Sarki Muhammadu Sanusi II ya yanke shawarar janye gudanar da hawan baki ɗaya, domin fifita rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano.

Tushen Takaddamar
Masarautar ta Kano dai tana ci gaba da fuskantar rarrabuwa a tsakanin ɓangarorin biyu wadanda ke gaban kotu domin tantance wanda ya kamata ya zauna a kan karagar mulkin.

Wannan dambarwa ta samo asali ne tun bayan da Alhaji Aminu Babba Ɗan-Agundi ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II, bisa korafin cewa ba a ba shi dama ta farkon fari ba, a matsayinsa na babban ɗan majalisar sarki lokacin da aka sake naɗa Sarki Sanusi na 16.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *