Mataimakin Gwamnan Katsina Faruk Lawal-Jobe ya ce babu wata hanya da ba ta biyuwa a fadin Jihar dalilin samuwar tsaro.
Mataimakin Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen bikin Hawan Sallah da ya gudana ranar Alhamis.
Babu hanyar da ba ta shiguwa saboda samuwar saukin matsalar tsaro,” inji shi.
Ya kara da cewa daga farkon gwamnatinsu zuwa yanzu, an samar da malamai sama da 7,000 don ganin an kara habaka harkar ilimi a dukkannin sassan jihar.
Da yake tsokaci a kan harkar noma, Faruk Lawal-Jobe ya bayyana irin shirye shiryen da Gwamnatin Jihar take samarwa ga manoma na fadin jihar domin su samu sauki tare da habbaka tattalin arzikin jihar baki daya.
A nasa jawabin, Sarkin Katsina Dokta Abdulmumini Kabir Usman ya yi kira ga al’umma da su hada kai tare da kauce wa hassada domin cigaban Jihar Katsina baki daya.