Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya yi kira ga dakarun Rundunar Tsaron Hadin Gwiwa ta Arewa ta Tsakiya (JTF-NC) dake karkashin shirin Operation Savannah Shield (OPSS) da su kara zage dantse wajen kakkabe ’yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuffuka da ke barazana ga zaman lafiya da tsaro.
Babban Hafsan ya yi wannan kira ne yayin da yake ganawa da sojoji a Barikin Sobi dake Ilori, a lokacin ziyarar aikinsa ta farko a Hedikwatar JTF dake Arewa ta Tsakiya.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, Kanar Appolonia Anele, ya sanyawa hannu ranar Alhamis, Janar Waidi ya jaddada cewa sojojin Najeriya na nan a shirye wajen cika aikinsu na doka da ya kunshi kare rayuka da dukiyoyi.
Ya kuma ce sojojin suna ci gaba da yaki don hana ’yan ta’adda samun damar cutar da fararen hula, da shiga al’umma ba tare da izini ba, ko kawo barazana ga tsaron kasa.
Ya kuma tabbatar wa sojojin cewa Rundunar tana samar da duk kayan aiki na yaki da kuma kayan aikin da ake bukata don kara inganta ayyukan tsaftace wurare da rusa mafakar ’yan ta’adda a jihohin Kwara da Neja.
Janar Waidi ya kara da cewa yana jajircewa wajen kula da walwalar sojoji da iyalansu, inda ya ce kyakkyawar kula da walwala suna da matukar muhimmanci wajen tabbatar da kwarin gwiwa da tasiri da kuma shirin yaki.
Ya yi kira ga sojojin da su kasance masu ladabi da nuna kwarewa da kuma biyayya ba tare da tangarda ba ga Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya da gwamnati
Tun da farko dai Kwamandan Operation Savannah Shield, Manjo Janar Y. Yahaya, ya nuna godiya ga COAS din saboda gaggauta kai dauki ga rundunar da samar da sabbin dabaru, da kuma goyon bayan da ake ci gaba da samu wajen kara karfin hadin gwiwar.
Ya tabbatar wa Babban Hafsan cewa sojojin za su ci gaba da kasancewa masu kwazo da nuna kwarewa da kuma jajircewa wajen cika aikin da aka dora musu na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin.
