Shari’ar da ake yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, kan zargin satar sauraron wayar Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro Nuhu Ribadu ta ci gaba a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Koda yake kamata yayi kotun karkashin Mai Shari’a Joyce Abdulmalik zata fara sauraron shaidu ne, sai dai lawyan DSS Oluwole Aladedoye (SAN) ya gabatarwa kotun korafin cewar iyalan El-Rufai na amfani da kafafen sada zumunta domin tunzuri da bata sunan fannin shari’a.
Barista Aladedoye ya shaida wa kotun cewa ‘yan uwan wanda ake zargi suna yawan amfani da kafafen sada zumunta da kuma tattaunawa da manema labarai domin nuna cewa hukumomin tsaro da masu shigar da kara suna tursasa wa El-Rufai ne kawai.
Lauyan ya buga misali da abin da ya faru ranar 15 ga watan Mayu, inda ya ce daya daga cikin matan El-Rufai ta isa ofishin Hukumar ICPC tare da masu daukar hoto inda ta dinga yada bidiyo kai-tsaye ta intanet, tana da’awar cewa ana hana mijinta abinci da kuma ganin iyalansa.
Sai dai lauyan El-Rufa’i, Barista E. E. Ekere, ya bayyanawa kotun cewar bashi da masaniya kan wadannan zarge-zarge, kuma bai ma kamata a dorawa El-Rufai alhakin abubuwan da mutane ke fada a wajen kotu ba. Duk da haka, ya yi alkawarin ba iyalansu shawara da su nuna juriya.
Yayin da take mayar da martani, Mai Shari’a Alƙali Joyce Abdulmalik ta bayyana cewa ba ta bibiyar kafafen sada zumunta, hasalima maganganun da akayi su a can, su tsaya a can, daga nan ta bayar da umarnin a ci gaba da shari’ar.
An Kalli Bidiyon “Hirar El-Rufa’i da Arise TV” A Cikin Kotu
Masu shigar da kara sun gabatar da shaida na farko da aka boye sunan sa saboda dalilai na tsaro da kuma na’urar “Flash Drive” da wata takarda, daga bisani Mai Shari’a ta bayar da umarnin kunna bidiyon wata hira da El-Rufai ya yi, da gidan talabijin na Arise TV a gaban kowa.
A cikin hirar, El-Rufai yana tattaunawa da mai gabatar da shiri, Charles Aniagolu, inda yake bayyana abin da ya faru da shi a filin jirgi, inda yace jami’an tsaro na farin kaya sun tunkare shi tare da mika masa goron gayyata zuwa ofishin su, amma kuma ya shaida musu cewar yana bukatar ganin sammaci a hukumance.
A cikin bidiyon, El-Rufa’i ya fadi cewar yana bibiyar wayar Mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro Malam Nuhu Ribadu-
“Mun saurari wayarsu, wani ne ya gano maganar wayar kuma ya shaida mana cewa shi (Ribadu) ne ya bayar da umarnin a kama ni. National Security Adviser ya shaidawa SSS cewa dole a sace ni a ranar. Kuma idan kayi yunkurin tafiya da mutum babu umarnin kotu wannan ba kamawa ba ne, garkuwa ce.” Inji El-Rufa’i
A cikin bidiyon, El-Rufai ya kuma ce ya yi aikin gwamnati na tsawon shekaru 16 kuma bai taba karbar rashawa ba, sannan ya kalubalanci ‘yan Najeriya da su fito su karyata shi idan karya yake.
Ya kuma yi zargin cewa shari’ar siyasa ce kawai saboda ya ki marawa yunkurin tazarce na Shugaba Bola Tinubu baya.
Tsayawar bidiyon ya sanya lauyan masu kara Barista Aladedoye neman kotun ta dage cigaba da sauraron shari’ar zuwa nan gaba, domin sake kawo cikakkiyar hirar, bukatar da Kotun ta amince ta dage zama zuwa Laraba 19 ga watan Mayu.
A ranar litin data gabata ne Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta bayar belin da tsohon gwamnan akan kudi naira miliyan 100, sai dai sharuddan da kotun ta gindaya ya sanya iyalansa gaza cimma karbar belin nasa.
A halin yanzu, El-Rufai na fuskantar shari’o’i da dama a Jihar Kaduna dangane da ayyukansa lokacin yana gwamna.
A watan da ya gabata ne wani alƙali a Kaduna ya hana bada shi beli tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a hannun hukumar ICPC. Wannan ya nuna cewa ko da wata kotun ta ba shi beli kan shari’ar satar saurarar waya, muddin kotun Kaduna ba ta soke umarninta ba, zai ci gaba da zama a tsare.