Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Babban Birnin Tarayya (FCT FA), Mouktar Mohammed, ya ce dole ne a gina harkar kwallon kafa a yankin a kan tubali mai dorewa a maimakon matakan agajin gaggawa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Malam Mouktar ya fadi haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Tsohon Filin Fareti (wato Old Parade Ground) da ke Gundumar Area 10.
Ya kuma amince cewa har yanzu ana fafutukar ganin Abuja ta samar da wata kungiyar kwallon kafa da za ta fafata a Gasar Firimiyar Najeriya (NPFL).
- Yadda Arsenal ta halalta wa kanta Kofin Firimiya na farko a shekara 22
- AFCON 2025: Wanne tasiri hukuncin Kotun Wasanni ta duniya zai yi?
- Bibiyar Wayar Ribadu: Kotu ta fara sauraron shaidu kan El-Rufa’i
“Ba za mu iya samar da hanyar shiga Gasar Firimiya da karfin tsiya ba; dole ne abin ya kasance cikin tsari mai dorewa,” inji shi.
Ya danganta wannan kalubale da rashin isassun masu daukar nauyi, da kuma mamaye gasar da kungiyoyin da gwamnatocin jihohi ke daukar nauyinsu suke yi, wadanda suke da karfin kudi fiye da na wasu.
Muhimmancin Masu Zuba Jari
Haka kuma ya yaba da bullar kungiyoyi masu zaman kansu a fagen kwallon kafar Najeriya, inda ya ambaci kungiyar Remo Stars a matsayin kyakkyawan misalin shiri na dogon lokaci da hakuri da kuma zuba jari.
“Cigaba mai dorewa yana bukatar masu zuba jari masu kishin gaske, wadanda suka fahimci tsarin wasan kuma suke a shirye su gina shi a hankali,” in ji shi.
Malam Mouktar ya kuma ce Hukumar tana ci gaba da yin nasarori a fannin kwallon kafa na matasa, da tsara gasar lig-lig, da kuma gasar kasa-da-kasa, duk da kalubalen karancin kudi da na abubuwan more rayuwa.
A cewarsa, Yankin Birnin Tarayya ya zama wata babbar matattara ga manyan kungiyoyin kwallon kafa na Najeriya da suka hada da Enyimba da Rangers International da Kano Pillars.
Ya kara da cewa, a karo na farko a tarihi, a bara Yankin ya karbi bakuncin wasan kusa da na karshe na Gasar Cin Kofin Kalubale (wato Federation Cup).
Mummunan Yanayin Filaye
Bugu da kari, Malam Mouktar ya yi kira da a samar da asusun harajin wasanni wanda zai tallafa wa cigaban wasanni daga tushe da abubuwan more rayuwa da kuma cibiyoyin horar da matasa a fadin kasar nan.
Ya nuna takaicinsa kan mummunan yanayin da wuraren wasanni suke ciki a fadin Abuja, yana cewa akwai ayyukan filayen wasa da dama da aka yi watsi da su a kananan hukumomin yankin, wadanda idan aka kammala su za su iya canza fasalin ci gaban wasanni.
Malam Mouktar ya kara da kashedi game da mayar da filayen kwallon kafa da na wasannin makarantu kasuwanni, lamarin da ya bayyana a matsayin barazana ga cigaban matasa da wasanni a matakin karkara.
“Dole ne mu kare filaye da wuraren wasanni. Idan babu abubuwan more rayuwa, cigaban kwallon kafa zai zama kusan abu mai wuya.
“Hukumar FCT FA tana ci gaba da kiyaye kyakkyawar dangantakar aiki da Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF) wajen karbar bakuncin wasanni da kuma inganta shirye-shiryen kwallon kafa na matasa a Abuja,” in ji shi.
