Mikel Arteta ya samar da wata sabuwar kungiyar kwallon kafa daga abin da ya gada a Arsenal

A karo na farko a shekara 22, kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta ciri tutar jagorancin harkar kwallon kafa a Ingila bayan ta lashe Gasar Firimiya ta kakar bana.

Kungiyar ta tabbatar da nasarar ne bayan Manchester City ta yi kunnen doki da Bournemouth.

Hakan ne ya sa Arsenal ta yi City din fintinkau da maki biyar.

Ta Kafa Tarihi

Mutane da dama sun nuna shakku a kan dorewar Arsenal a saman tebur duk da rawar da ta taka a wannan kakar.

Sai dai daga karshe ta bai wa marada kunya.

A hanyarta ta kaiwa wannan matsayi, Arsenal ta yi nasara a wasanni 28—fiye da na “Invincibles” na Arsène Wenger a 2003/2004—kuma ta nuna ƙarfin hali a ƙarshen kakar.

Bayan shan kashi a hannun Manchester City a watan Afrilu, Arteta da ’yan wasansa suka dawo da karfi, suka yi nasara a wasanni hudu a jere ba tare da an zura musu ko da kwallo daya ba, ciki har da nasara mai uhimmanci ta 1-0 a kan Burnley.

Dabarun Bugun Tazara

Ɗaya daga cikin makaman Arsenal shi ne ƙwarewarta wajen amfani da dabarun bugu ana cikin wasa (set-piece a Turance).

Wadanan sun hada da bugun kusurwa (wato corner kick a Turance) da bugun tazara (wato free kick a Turance) da bugun daga-ka-sai-mai-tsaron-gida (wato penalty kick a Turance) da jifa (wato throw in a Turance) da sauransu.

Ta kafa sabon tarihin Gasar Firimiya wajen yawan cin kwallaye daga kusurwa, inda ta zura kwallo 19.

Wannan ya taimaka mata wajen yin nasara a wasanni masu wahala.

Tatatar Arteta

Ga Mikel Arteta, wannan nasara ta fi komai. Bayan ya lashe FA Cup a 2020 da Community Shield sau biyu, yanzu ya shiga jerin manyan masu horar da Arsenal wadanda suka ɗaga kofin Gasar Firmiya.

Duk da tatatar da ta yi fama da shi a wasu lokuta, dabarunsa da kuma yadda ya gina kwarin gwiwa a matasan ‘yan wasa sun sake fasalin kungiyar.

Arteta ya kawo wani sabon tsarin wasa, inda ya haɗa tsaurara tsaro da saurin kai hari.

Wannan ya ba Arsenal damar yin nasara a kan manyan ƙungiyoyi da kuma guje wa rasa maki a ƙananan wasanni.

Ya kuma gina ƙungiya mai dogaro da matasa kamar Bukayo Saka da Martin Ødegaard, tare da haɗa su da gogaggun ’yan wasa.

Sannan ya yi fice wajen ƙarfafa kwarin gwiwa da ɗabi’ar nasara – misali, bayan kashin da suka sha a hannun Manchester City, ya motsa ’yan wasansa sun dawo da karfi.

Manchester City Ta Yi Rauni

Manchester City ta Pep Guardiola, wadda take neman sake lashe Gasar Firimiya, ta yi rauni a lokacin da take bukatar karsashi.

Gajiya da kuma rashin tabbas game da makomar Guardiola sun yi tasiri, sannan kunnen dokin da suka yi da Bournemouth ya ba Arsenal damar lashe kofin.

Tarihi Da Makoma

Wannan nasara ce babbar nasara ta farko da Arsenal ta yi a cikin shekaru shida, kuma Gasar Firmiya ta farko da ta lashe tun bayan kakar da aka yi muku lakabi da Gagarabadau, wato Invincibles a Turance.

Nasarar ta kara muhimmanci ne ganin yadda Arsenal din ke fatan samun nasara uku yayin da take shirin fafatawa a wasan karshe na Gasara Zakarun Turai da Paris Saint-Germain nan gaba a wannan watan.

Yayin da magoya bayan Arsenal suke murna da wannan sakamako, mai yiwuwa tunainsu shi ne “mahukurci mawadaci”: a yau kungiyar ta dare kololuwar harkar kwallon kafa ta Ingila.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *