Kotun ECOWAS ta baiwa Najeriya umarnin rage cunkoso a gidajen Gyaran halin Kasar [ECOWAS COURT]

Kotun ECOWAS ta umarci Najeriya ta gaggauta daukar matakin rage cunkoso a gidajen gyaran halin kasar, tare da mika mata cikakken rahoto kan matakan da aka dauka a cikin watanni shida masu zuwa.

A wani hukuncin da ta yanke ranar 15 ga watan Mayun 2026, Kotun ta ce ci gaba da tsare wadanda ake zargi ba tare da shari’a ba, da mummunan cunkoso a gidajen yari, ya saba da yarjejeniyar mutunta haƙƙin dan’Adam da Najeriya ta sanya wa hannu.

Tun da farko wata Kungiya mai zaman kanta ta mai suna “Centre for Community Law” ce ta shigar da karar, inda ta koka cewar mafi yawancin mutanen da ke tsare a gidajen yarin Najeriya na jiran hukunci ne.

Karar mai lamba ECW/CCJ/APP/05/25, ta dogara ne da hujjojin cewar tsarewar da ake yiwa wadanda ake zargi a Najeriya tamkar take musu wasu haƙƙoƙine, na shafe tsawon lokaci a tsare ba tare da shari’a ko bayar da belin su ba.

Masu shigar da karar sun bayyanawa kotun cewar sama da fursunoni dubu 79 da ke tsare, fiye da mutum dubu 52 na jiran shari’a ne, lamarin da masu karar ke dangantawa da ‘cikakkiyar shaidar gazawar tsarin shari’a da na gyaran hali a kasar’.

Sai dai Najeriya ta kalubalanci ikon da kungiyar take dashi na kai ta kara, sannan ta musanta zarge-zargen bisa hujjar ta na gudanar da ayyukan ta ne bisa tsarin da doka ta tanadar. Najeria tace gidajen gyaran halin ta suna da kayan aiki da suka dace.

Sai dai Kotun ECOWAS ta yi watsi da hujjojin da Kasar ta gabatar, tana mai cewa  lamarin ya saba wa alkawuran da Najeriya ta dauka na kiyaye ka’idojin kare hakkin dan’adam na kasa da kasa.

A karshe Kotun tace kungiyar na da dukkanin damar shigar da Najeriya kara a gabanta, bisa la’akari da koyarwar (actio popularis), wanda ya baiwa kungiyoyi damar shigar da kara domin kare muradan al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *