’Yan Majlisar Wakilai da dama ne suka kasa kai bantensu a yunkurin da suka yin a komawa Majalisa badi a inuwar jam’iyyar APC.
Sakamakon zabubbukan fitar da gwanin da aka gudanar a karshen mako ne ya bai wa ’yan majalisar mamaki.
A cikin ’yan majalisar da aka kwarfe din har da wadanda suka dade suna jan zarenu da ma wasu daga cikin shugabannin Majalisa.
- Kotu ta gindaya tsauraran sharudda don ba da belin El-Rufai
- Abin da ya kai ni gidan Shugaban Jam’iyyar APC –Wike
- APC ta ƙara wa’adi ga masu neman takara
Wadannan ’yan majlaisa su ne:
Fulogan Majalsa
Julius Ihonvbere

Honorebul Julius Ihonvbere ne Shugaban Masu rinjaye a Majalisar ta Wakilai – ma’ana, shi ne mutum na uku mafi girman mukami a Majalisa.
Ya yi rashin nasarar karbar tikitin APC din don sake wakiltar Mazabar Owan ta Gabas/Owan ta Yamma a Jihar Edo a karo na uku.
An ca ya sha kashi ne a hannun tsohon Kwamishinan Ma’adinai Andrew Ijegbai, yayin da ake radi-radin samar da tsarin karba-karba a tsakanin kananan hukumomin Owan ta Gabas da Owan ta Yamma.
Sai dai dan majalisar ya musanta rahotannin cewa ya sha kaye, inda ya fitar da wata sanarwa mai dauke da abin da ya kira “hakikanin sakamakon zaben”.
Yusuf Gagdi

Rahotanni sun ce Honorebul Yusuf Gagdi, mai wakiltar Mazabar Pankshin/Kanke/Kanam kuma Shugaban Kwamitin Majalisa mai Kula da Rundunar Sojin Ruwa, ya rasa damar komawa Majalisar.
A zeben fitar da gwanin da aka gudanar, Dokta John Tongshinen ne ya hana Honorebul Gagdi tsayawa a karkashin inuwar APC bayan ya laukme kuri’u 29,968 yayin da dan majalisar mai ci ya samu 5,849 kacal.
An dade ana yi…
Nicholas Mutu
In dai bay a samu tikitin wata jam’iyya kafin zabubbukan 2027 ba, Honorebul Mutu yana ji yana gani zamansa a Majalsa na shekaru masu zai zo karshe bayan da hakarsa ta sake wakiltar Mazabar Bomadi/Patani a Jihar Delta ta kasa cimma ruwa.
An bayar da rahoton cewa tun 1999 Honorebul Mutu yake wakiltar mazabarsa a Majlisa.
An ce Barista Basil Okolobaowei Ganagana ne ya taka wa Honorebul Mutu birki.
Esosa Iyawe
An zabi Honorebul Esosa Iyawe ne a karkashin tutar jam’iyyar LP a 2023, ya kuma sauya sheka zuwaAPC daga baya.
An ce wani tsohon Kwamishinan Ilimi ne ya kayar da shi a Mazabar Oredo ta Jihar Edo.
Sai dai dan majlisar ya ki amincewa da sakamakon zaben, yana mai cewa an kori magoya bayansa.
Mansur Musa Jega
Dan majlisa mai wakiltar Mazabar Jega/Gwandu/Aleiro ta Jihar Kebbi ya rasa tikitin jam’iyyar ta APC ga tsohon Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Halu Jafar Ahmed Jega sakamakon ittifakin da bangarorin masu hamayya suka yi.
Ismail Kayode
Shi kuwa Ismail Kayode, wanda ke wakiltar Mazabar Ifelodun/Oyun/Offa ta Jihar Kwara ya rasa tikitin ne bayan ya sha kaye a hannun tsohon Sakataren Yada Labarai na Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, Rafiu Ajakaye.
Da sauran su…
Sauran ’yan majalisar da ba su kai labari ba sun hada da:
’Yan Mjalaisa hudu daga Jihar Jigawa:
Muktar Muhammad, dan majalisa mai wakiltar Mazabar Kazaure/Roni/Gwiwa/Yankwashi;
Ibrahim Usman Auyo, dan majalaisa mai wakiltar Mazabar Hadejia/Auyo/Kafin Hausa;
Sa’adu Wada Taura, dan majalisa mai wakiltar Mazabar Ringim/Taura; da kuma
Yusif Sa’idu Miga, dan majalisa mai wakiltar Mazabar Jahun/Miga.
A jIhar Imo ma ’yan majalsa hudu aka kwarfe; su ne:
Matthew Nwogu, dan majalisa mai wakiltar Mazabar Aboh Mbaise/Ngor Okpala;
Miriam Onuoha, ’yar majalisa mai wakiltar Mazabar Okigwe ta Kudu;
Harrison Nwadike, dan majalisa mai wakiltar Mazabar Isu/Njaba/Nkwerre/Nwangele; da kuma
Emeka Martins Chinedu, dan majalisa mai wakiltar Mazabar Ahiazu/Ezinihitte.