Wike yace ziyarar da ya kaiwa Shugaban APC na kasa ta biyan bashi ce

Ministan Birnin Tarayya Nyesom Wike ya mayar da martani ga masu sukar ziyarar da ya kai wa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Farfesa Nentawe Yilwatda.

Wike ya bayyana cewa ziyarar da ya kaiwa Yilwatda ta abota ce, don haka bai kamata a siyasantar da ita ba.

Ya fadi hakan ne a ranar Laraba yayin da yake duba ayyukan hanyoyi a yankunan Karu, Apo-Karshi, da Kubwa da ke Abuja, inda yace “Abota ba Gaba ba ce”

“Duk da cewa abokan aiki ne mu kafin ya zama shugaban APC, Shin idan na ganshi labewa zan yi?” — inji Wike

Ministan ya bayyana cewa shugaban na APC ya sha kokarin kawo masa ziyara sau da dama amma hakan bai samu ba, saboda haka wannan ziyarar tasa tamkar rance ne ya biya.

Ko da yake, Wike ya ce ba shi da hurumin bayar da bayani dalla-dalla ga  kan mutanen da yake gani a sirrance. A cewarsa, bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya zama silar gaba a tsakanin mutane ba.

Duk da cewa Wike yana rike da mukamin Minista a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, har yanzu yana ikirarin kasancewa dan jam’iyyar hamayya ta PDP ne shi.

A karshe, Ministan ya ce hankalin sa ya karkata ne kacokan kan gina ababen more rayuwa ga mazauna Abuja, maimakon bata lokacin sa wajen sauraron surutan ’yan siyasa marasa ma’ana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *