Takaddama ta barke a Phillipines game da dalilin harbe-harben bindiga a ginin Majalisar Dattawan kasar.
Sakataren Majalisar, Mark Llandro Mendoza, ya shaida wa manema labarai cewa jami’an Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Kasa (NBI) ne suka yi harbin yayin da suka yi kokarin shiga ginin.
Sai dai Shugaban Hukumar ta NBI ya musanta hakan, yana cewa ba su tura jami’ai Majalisar ba.
- Yadda ficewar UAE daga OPEC ka iya girgiza harkar danyen mai
- Iran ta gindaya wa Amurka sharadi game da nukiliya
- Amurka ta toshe tashoshin jiragen ruwan Iran
BBC ta ruwaito cewa an ga ‘’yan sanda da sojoji suna sintiri a harabar Majalisar rike da bindigogin da suke Kallon kasa.
Me ya kai fura zani?
Wannan takaddama dai ta samo asali ne daga umarnin da Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya (ICC) ta bayar na kamo mata wani dan majalisa kuma tsohon shugaban Rundunar ‘’Yan Sanda ta Phillipines din, Sanata Ronald dela Rosa.
Kotun tana neman Dela Rosa ne bisa tuhumar kashe gomman mutane lokacin yana shugabantar rundunar ’yan sandan, inda ya jagoranci yakin da tsohon Shugaban Kasa Rodrigo Duterte ya daura da miyagun kwayoyi a tsakanin 2016 da 2018.
An dubban mutanen da ake zargin dillalan miyagun kwayoyi da kananan masu kasuwancinsu ne aka kashe.
Kungiyoyin kare hakkin bil’Adama kuma sun ce galibin wadanda aka zarga an kashe su ne ba tare da shari’a ba.
Abin da ya faru
An bayar da rahotn cewa da maraicen ranar Laraba Sanata Dela Rosa ya hau Facebook inda ya yi Magana kai-tsaye yana cewa ya samu labarin hukumomi za su kama shi.
“Ina neman taimakonku: kada mu bari a sake gurfanar da wani dan kasar Philippines a Hague kamar yadda aka garfanar da Shugaba Duterte”, inji dan majalisar.
Kusan sa’a guda bayan nan ne aka ji harbe-harben, wadanda aka ce a haw ana biyu na benen majalisar aka jiyo kararsu.
Dela Rosa dai ya nemi mafaka a Majalisar Dattawan sannan ya bukaci Kotun Kolin kasar ta haramta wa hukumomi aiwatar da umarnin na ICC.
Sai dai Kotun Kolin ta ki haramta kama Sanata Dela Rosa; a maimakon haka, ta bai wa Gwamnatin Shugaba Ferdinand Marcos sa’o’i 72 ta mayar da martini ga bukatar dan majalisar.
Siyasar Phillippines
Dela Rosa yana cikin manyan na hannun daman tsohon Shugaba Duterte.
Bayan ya yi ritaya daga shugabancin Rundunar ’Yan Sanda Duterte ya nada shi shugaban Hukumar Gidajen Yari.
Shekara gida bayan nan kuma ya tsaya Takara a zaben Majalisar Dattawa ya kuma yi nasara.
Ranar Litinin Majalisar Wakilai ta tsige Mataimakiyar Shugaban Kasa Sara Duterte (wacce ’ya ce ga tsohon Shugaban Kasa Duterte) bisa zargin almundahana da yin barazana ga Rayuwa Shugaban Kasa Marcos.
Sai dai tsigewar ba za ta tabbata bai sai Majalisar Dattawa ta amince – idan ta tabbatar da lamarin to za a haramta wa Sara Duterte tsyawa takarar shugaban kasa a 2028.
Ranar da aka yi harbe-harben ne kuma aka kai takardun da suka shafi batuun Majalisar ta Dattawa.
Kasancewar Dela Rosa a Majalisar Dattawan a wannan makon ya taimaka wajen zaman Sanata Alan Peter Cayetano, wanda tsohon Ministan Harkokin Waje ne a Gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Duterte, Shugaban Majalisa.
Hakan ya sa ’yan majalisar da suke da alaka da Shugaban Kasa Ferdinand Marcos sun zama marasa rinjaye rinjaye.
