Hoto: Ma'aikatar harkokin wajen Iran

Ma’aikatar Harkokin Waje ta Iran ta yi watsi da bukatun Amurka game da makomar tattalin arzikinta, tana zargin hukumomi a Washington da yunkurin yi mata ingiza-mai-kantu-ruwa.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen ta Iran Esmaeil Baghaei ne ya bayyana matsayar kasarsa game da makomar tattaunawar nukiliya da kuma alaka da kasar Amurka a yayin wani taron manema labarai da ya gudana ranar Laraba a birnin Tehran.

Baghaei ya jaddada cewa Iran ba ta taba tashi daga teburin tattaunawa ba,  kuma a shirye take ta koma kan teburin tattaunawa idan har sauran kasashen za su mutunta yarjejeniyar shekarar 2015,  kuma su janye takunkuman da aka sanya wa al’ummar Iran ba kakkautawa.

“Amurka ce ta fice daga yarjejeniyar, saboda haka ita ce ya kamata ta nuna gaskiyarta wajen gyara kura-kuranta.”

Baghaei ya yi gargadin cewa matsin lambar da Amurka ke yi wa Iran ta hanyar kawayenta a yankin Gabas ta Tsakiya ba zai zama alheri ba.

Ya kara da cewa tsaro zai tabbata ne kawai idan kasashen da suke yankin suka hada kai ba tare da tsoma bakin kasashen ketare ba.

Ya jaddada cewa Iran ba za ta taba mika wuya ga takunkuman tattalin arziki ba, kuma za ta ci gaba da amfani da hanyoyin diflomasiyya domin kare hakkokinta na bunkasa fasahar nukiliya ta zaman lafiya.

Masu sharhi na ganin kalaman Baghaei a matsayin wani sako na “takala” ga Amurka, inda Iran ke nuna cewa ba za ta amince da tattaunawar da ba za ta amfani tattalin arzikinta ba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke fuskantar kalubalen tsaro a yankin Lebanon da Gaza, wadanda ke shafar alakar Iran da manyan kasashen duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *