Ranar Juma’a Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya bar China bayan ziyarar da ya kai ta kwana biyu.
Trump ya yi ikirarin cewa shi da Xi Jinping sun “kawo karshen matsaloli da dama wadanda wasu mutanen ba za su iya cimmawa ba” yayin ziyarar.
Ya kuma hakikce cewa akwai danganataka “mai karfi” a tsakaninsa da Xi, yana cewa sun cimma abubuwan ban mamaki.
- Amurka ta toshe tashoshin jiragen ruwan Iran
- ‘Abin da ya sa za mu kera motoci masu amfani da lantarki a Abuja’
- Iran ta gindaya wa Amurka sharadi game da nukiliya
“Mun tattauna a kan Iran, kuma ra’ayinmu ya zo daya – muna so a kawo karshen yakin kuma ba ma so mu mallaki makamin nukiliya….
“Amma mun tattauna wasu abubuwa da dama kuma ina ganin mun yi ittifaki sosai”, inji Trump.
Ta fi babu….
Sai dai kuma a wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajenta ta wallafa a shafinta na X, China ba ta tabbatar da abubuwa da dama da Amurka ta ce an cimma matasaya a kai ba.
Hasali ma masharhanta da dama suna ganin har yanzu akwai bambance-bambance da dama a tsakanin kasashen musamman a kan batutuwan da suka shafi yakin Iran.
Game da cinikayya ma, duk da manyan ‘’yan kasuwar Amurka da shugabannin manyan kamfanoni da suka yi wa Trump rakiya, masana suna ganin yarjejeniyoyin da aka kulla da suka shafi kasuwanci da tattalin arziki ba su taka kara sun karya ba.
Masana suna ganin wannan ziyara ta fi mayar da hankali ga nuna bajinta da al’adu, amma babu wasu cikakkun bayanai game damanufofin da bangarorin biyu suka amince da su.
Bude ido
Ziyarar ta Mista Trump dai ta kammala ne da rangadi a Zhongnanhai, wani katafaren rukunin gine-gine na karni na 14 mai tsaro sosai, inda manyan shugabannin China suke zaune kuma suke gudanar da ayyukansu.
A baya ma wasu shugabannin Amurka sun ziyarci wannan rukunin gine-gine, ciki har da Barack Obama da George W. Bush da kuma Richard Nixon a lokacin ziyararsa mai cike da tarihi a shekarar 1972.
Yayin rangadin Trump, ya yaba da wasu “kyawawan furannin da babu kamarsu” da kuma wasu bishiyoyi, wadanda Xi ya ce sun kai shekara 200 zuwa 400.
“Haka suka dade a tsaye?” Trump ya tambayi Xi.
“Haka ne, akwai ma bishiyoyi masu shekaru 1,000 a wasu wuraren,” in ji Xi.
China da Iran
China ce kasar da ta fi kowa sayen danyen man Iran, kuma ita ce babbar abokiyar cinikayyarta.
Don haka ne ma gwamnatin Trump ta sanya ran cewa Xi zai yi amfani da wannan tasiri na tattalin arziki da siyasa domin matsa wa Iran lamba ta hau teburin shawarwari.
Trump ya ce China ta amince ta sayi danyen man Amurka, da jiragen sama na Boeing guda 200, da kuma “kayayyakin gonakinmu da dama”— amma Ma’aikatar Harkokin Wajen China ta kauce wa amsa tambayoyi game da yarjejeniya a kan kayan gona da batun sayen jiragen na Boeing.
