Taron na kwanaki biyu da Ministocin Harkokin Wajen ƙasashe membobin ƙungiyar BRICS suka halarta a birnin New Delhi na ƙasar Indiya ya kammala a ranar Juma’a ba tare da cimma matsaya guda kan yaƙin Amurka, Isra’ila da kuma Iran ba.
Ministan Harkokin Wajen Indiya, Subrahmanyam Jaishankar ya jagoranta, ya gudana ne a daidai lokacin da yaƙin Iran ya shiga rana ta 77.
Babban abin da ya fi ɗaukar hankali a taron shi ne musayar kalamai masu zafi tsakanin Ministan harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi, da wakilin Hadaddiyar Daular Larabawa Khalifa bin Shaheen Al Marar.
Abbas Araghchi ya buƙaci BRICS ta yi Allah wadai da hare-haren Amurka da Isra’ila akan Iran, inda ya zargi Hadaddiyar Daular Larabawan da bai wa Amurka damar amfani da sansanin soji domin kai wa Iran hari.
Araghchi yace su na da hannu dumu-dumu a hare-haren da ake kai wa Iran, har ma da wani hari da aka kai wa wata makaranta a birnin Minab inda ɗalibai 170 suka rasu.
Da yake martini kan matsayin Tehran, Wakilin Hadaddiyar Daular Larabawa Khalifa Bin Shaheen Al Marar ya yi watsi da zarge-zargen, inda ya bayyana cewa Iran ce ke kai hare-hare kan fararen hula da tashoshin makamashi a ƙasarsu.
Al Marar ya ce dakarun su sun kakkabo jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami sama da 2,800 da Iran ke harbo musu, kwanaki 77 da fara yakin.
Ganin yadda takaddama mai zafi ta kaure a tsakanin kasashen biyu, Ministan Harkokin Wajen Indiya, S. Jaishankar dake shugabantar taron ya shiga tsakani a wani yunƙuri na samar da daidaito. Har yayi kiran da a tabbatar da tsaro a hanyoyin jiragen ruwa na ƙasa da ƙasa.
“Sanya takunkumi na gefe ɗaya ba zai maye gurbin tattaunawa ba, kuma matsin lamba ba zai taba zama madadin diflomasiyya ba.” Inji Jaishankar.
Sauran ƙasashen da suka halarci taron sun haɗa da Rasha, Brazil, Afirka ta Kudu, Indonesia, Masar da Habasha. Ita kuwa ƙasar China, jakadanta ne ya wakilce ta sakamakon ziyarar Shugaba Donald Trump na Amurka zuwa birnin Beijing a daidai lokacin taron.
Wannan shi ne karo na biyu a jere da taron BRICS a ƙarƙashin jagorancin Indiya ya gagara cimma matsayi guda kan rikicin, da ya shafi Amurka da Isra’ila da kuma Iran.
Ana sa ran shugabannin ƙasashen BRICS goma za su gudanar da babban taron ƙololuwa a watan Satumba mai zuwa a ƙasar Indiya, inda ake fatan za a sake tattaunawa kan hanyoyin samar da zaman lafiya a duniya.
