Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce dakarun ƙasarsa da haɗin gwiwar sojojin Najeriya sun kawar da “ɗan ta’adda mafi hatsabibanci a duniya.

Mista Trump ya bayyana haka ne a shafinsa na Truth Social da safiyar ranar Asabar.

“Abu-Bilal al-Minuki, wanda shi ne mutum na biyu mai girman matsayi a ƙungiyar ISIS a duniya, ya yi zaton zai iya ɓuya a Afirka.

“Sai dai bai san cewa muna da majiyoyi da suke labarta mana duk abin da yake yi ba“, inji Trump.

Kisan, a cewarsa, zai raunana ISIS a faɗin duniya.

Shugaban na Amurka ya kuma gode wa Gwamnatin Najeriya bisa goyon bayan da ya ce ta bayar don samun nasarar harin.

Da take tabbatar da harin a wata sanarwa da ta wallafa a soshiyal midiya, Hedkwatar Tsaro, wadda ta ce harin wani ɓangare ne na ƙawancen da ƙasashen suka ƙulla na musayar bayanan sirri, ta kwatanta al-Minuki da cewa shi ne ƙashin bayan ayyukan ISIS na musamman.

“Abu-Bilal al-Minuki ƙusa ne a ISIS wanda ya kasance yana jagoranci a kan al’amuran da suka shafi yaɗa labarai da yaƙi a kan tattalin arziƙi da kuma ƙirƙirar makamai da abubuwa masu fashewa da jirage marasa matuƙa.

“Mutuwarsa za ta toshe wata muhimmiyar kafa da ISIS take amfani da ita shirya da tsara ayyukanta a faɗin duniya”, inji sanarwar mai ɗauke da sa-hannun Daraktan Yaɗa Labarai, Manjo Janar Samaila Uba.

Sanarwar ta ƙara da cewa harin ya nuna ƙudurin rundunonin tsaron Najeriya na kawar da ta’addanci da kayan aikin ‘yan ta’adda don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya da Afirka ta Yamma.

Ko a watan Disamba na bara ma dai Amurka ta ƙaddamar da hari a wani yanki na Jihar Sakkwato, inda ta ce akwai sansanin ’yan ta’adda.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *