Rundunar sojin Najeriya ta ce babub wata hujja da take tabbatar da mutuwar fararen hula sakamakon wani hari da ta kaddamar ta sama a kan ’yan bindiga a Jihar Zamafara.
Daraktan Yada Labarai na Hedkwatar Tsaro, Manjo Janar Michael Onojo, ya bayyana haka.
“Babu wata kwakkwarar hujja da aka samu ta wata sahihiyar majiya ta hukuma ko mai zaman kanta da take tabbatar da mutuwar fararen hula”, inji Janar Onoja.
- Yadda ‘kisan’ tsohon dan majalisa daga Jigawa ya firgita mutanen Abuja
- Dakarun Operation Haɗin Kai sun daƙile hari a Benisheik
- Ya kamata Tinubu ya farka daga barci –Atiku
Daraktan Yada Labaran ya kara da cewa an yi la’akari da dokokin kasa-da-kasa wajen kai harin bayan samun sahihan bayanan sirri cewa wasu manyan jagoroin ’yan ta’adda sun taru a wurin.
Ranar Talata ne dai kungiyar kare hakkin bil’Adama ta Amnesty International ta fitar da wani rahoto da yake cewa fararen hula akalla 100 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon wani hari da rundunar sojin sama ta kai a kan wata kasuwa da ke makare da jama’a a kauyen Tumfa, tana kira da a gudanar da bincike.
“Wajibi ne hukumomi sun binciki wannan mummunan harin ta sama su kuma kawo karshen hare-haren ganganci da ake kai wa fararen hula.
“A sasssan Arewacin Najeriya masu fama da rikice-rikice, fararen hula suna dandana kuda fiye da kima; [don haka] wajibi ne a daina kawar da kai daga wadannan mace-mace marasa kyawun gani”, inji Amnesty.
Kungiyar agaji ta Red Cross ma ta bayar da rahoton mutuwar fararen hula yayin harin, wanda aka kai ranar Lahadi.
Sai dai Manjo Janar Onoja ya yi bayani cewa ko da yake akwai kalubale wajen tabbatar da gaskiya a irin wannan lamari, nazarin da runudnar ta gudanar ya nuna cewa an yi nasarar kawar da ‘’yan ta’adda da dama.
Ba wannan ba ne karo na fark oba da kungiyoyin kasa-da-kasa suke zargin rusnunar sojin Najeriya da kaddamar da hare-hare a kan fararen hula.
Ko a watan jiya ma kungiyar Amnesty ta yi zargin cewa an kai hari a kan fararen hula yayin da suke ci kasuwa a wani kauye da ke kan iyakar Jihohin Borno da Yobo.
Sai dai kuma Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce gwamnatinsa ta dade da rufe kasuwar.
