Sojojin Operation Hadin Kai sun ce sun daƙile wani mummunan farmakin ‘yan ta’adda a Benisheikh a Jihar Borno.

Dakarun runduna ta 29 a ƙarƙashin rundunar ta Operation Hadin Kai sun ce sun fuskanci wani hari ne a kan helkwatarsu.

A wata sanarwa da ya fitar, Dataktan Yaɗa Labarai na Rundunar, Manjo Janar Michael Onoja, ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na daren Alhamis, inda maharan suka yi yunkurin kutsawa cikin sansanin sojin.

Sanarwar ta ce dakarun, a karkashin jagorancin Birgediya Janar Oseni Braimah, sun nuna jarumta da kwarewa, inda suka yi amfani da manyan makamai wajen fatattakar maharan.

Sakamakon martanin da sojojin suka mayar cikin tsari, ‘yan ta’addan sun tsere cikin rudani tare da barin dabarunsu na baya, inji sanarwar.

Wannan hari ya nuna yanke kauna da ‘yan ta’addan suka yi bayan asarar da suka yi a hare-haren baya-bayan nan, wadanda suka sa suke kai hare-hare marasa galihu kan sansanonin soji a cewar Onoja.

Koda yake an rasa ran wasu jaruman sojoji yayin gudanar da wannan aiki, rundunar ba ta bayyana sunayensu ba.

Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede, ya jinjina wa jarumtar wadannan sojojin, yana mai cewa sadaukarwarsu za ta ci gaba da zama abin alfahari ga kasar nan.

Rundunar sojin ta ce tana rokon jama’a da kafafen yaɗa labarai da su ba ta sarari domin sanar da ‘yan uwan sojojin da suka rasu kafin bayyanar ƙarin bayanai, kamar yadda tsarin aikin soja yake.

Ko da yake ta bukaci al’umma su guji labaran ƙanzon kurege, ta hanyar kauce wa bayanai da ba a ji daga bakinta ba.

Wasu bayanai dake yawo a kafafen sada zumunta na nuni cewa ƴan ta’addar sun yiwa rundunar ɓarna, ta hanyar kashe mata wani babban jimi’i da wasu ƙananan sojoji.

A baya bayan dai ƴan ta’addan na kaiwa sansanonin sojin hare hare masu zafi, matakin da masana tsaro ke cewa bai kyautu rundunar ta zauna ana kawo mata hari har gida ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *