Shugabannin tsagin Kabiru Tanimu Turaki na PDP sun ce sun kai wa takwarorin aikinsu na ADC ziyara ne don nuna goyon baya a gare su (Hoto: Facebook/PDP)

Shugabannin jam’iyyar hamayya ta PDP sun kai ziyarar nuna goyon baya ga takwarorin aikinsu na jam’iyyar ADC, bayan abin da suka kira da hare-haren siyasa da ake kai wa jam’iyyun hamayya a Najeriya.

A yayin ziyarar, PDP ta bayyana damuwarta kan barazanar da ta ce jam’iyyun hamayya suna fuskanta baki daya, inda ta nuna cewa ita kanta halin da take ciki ke nan.

Tawagar ta jaddada bukatar kasancewa cikin shiri da sanya ido a kan duk wani mataki da ka iya raunana tsarin dimokuradiyya da kuma ’yancin jam’iyyu da dama a kasar nan.

Shugabannin PDP din da suka kai ziyarar sun haɗar da Gwamna Seyi Makinde da Kabiru Tanimu Turaki SAN, da kuma Sanata Adolphus Wabara.

Sauran su ne Farfesa Jerry Gana da tsohon Gwamnan Jihar Neja Babangida Aliyu da Janar Ishaya Bamayi mai ritaya.

A nata ɓangaren, jam iyyar ADC ta ce dimokuraɗiyyar ƙasar nan na fuskantar babbar barazana, musamman a yadda ake yin zagon ƙasa ga manyan jam’iyyun hamayya domin raunana su.

Bangarorin biyu sun amince da bukatar ci gaba da tuntubar juna da hadin gwiwa domin kare martabar dimokuradiyya da cibiyoyin da suka gina ta.

Yanzu haka dai jam’iyyun biyu suna fama da rikicin shugabanci da rarrabuwar kawuna, inda bangarori daban-daban suke fuskantar juna a kotu.

Jam’iyyun dai na zargin jam’iyyar APC mai mulki da Gwamnatin Tarayya da kitsa rikice-rikicen, amma a lokuta daban-daban sun sha musanta hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *