Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta ƙaryata rahotannin da ake yaɗawa cewa shugabanta, Sanata David Mark, ya yi murabus.

A wata sanarwa da ta fito daga ofishinta na yaɗa labarai, ADC ta bayyana rahoton a matsayin ƙirƙirarre, wanda wasu marasa kishin ƙasa masu yaɗa farfaganda suka kitsa.

Jaridar Blueprint ta ruwaito sanarwar tana cewa har yanzu Sanata David Mark ne halattaccen Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, kuma ba shi da wani nufi na barin kujerarsa.

Jagorancin ADC ya jaddada cewa jam’iyyar tana nan tsintsiya maɗaurinki ɗaya, tana mai da hankali da sadaukarwa wajen inganta ɗabi’un dimokuradiyya da shugabanci na gari a Najeriya.

Haka zalika, jam’iyyar ta yi gargaɗi game da duk wani yunƙuri na ruɗa mambobinta, inda ta ɗora alhakin hakan kan tsoron da wasu ke da shi na ganin yadda darajar ADC ke ƙara ƙarfafa gabanin babban zaben shekarar 2027.

Daga nan ADC ta buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da aminta da shugabancin jam’iyyar da kuma zaman lafiyar da ake da shi a cikinta.

Idan ba a manta ba wata taƙaddamar shugabanci da ta kunno kai a jam’iyyar ta sa a makon jiya Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta cire sunan Sanata David Mark da Ogbeni Rauf Aregbesola a matsayin Shugaba da Sakataren ADC na Ƙasa daki-daki daga kundin bayananta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *