Fitaccen dan fafutuka kuma tsohon dan Majalisar Dattwa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi jirwaye mai kamar wanka kan dambarwar da ake yi a jam’iyyar ADC, inda ya kwatanta shiga tsohuwar jam’iyya da sayen tsohuwar mota.
A yayin da rikicin shugabanci ke kara ruruwa a jam’iyyar ta ADC, Sanata Shehu Sani ya yi amfani da shafinsa na X wajen yin misali da kalubalen da ke tattare da gadon tsohon tsarin siyasa maimakon gina sabo.
A cewarsa, matsalar inji da birki su ne manyan misalai da za ka yi wa duk mai sayen toshuwar mota, misali ne da ke kan duk wanda ya zabi ya shiga ko ya gaji tsohuwar jam’iyya, to ya shirya wa gyara.
“Idan ka sayi tsohuwar mota ko ka gaje ta, dole ne ka fuskanci matsalolin da suka shafi inji, birki, tayoyi, shaf, filta da sauran su. Wannan shi ne ainihin halin da ake ciki a ADC.”
Shehu Sani ya kara da cewa akwai babban bambanci tsakanin wanda ya yi rajistar sabuwar jam’iyya da wanda ya je ya kwashi tsohuwar mai dauke da tsofaffin korafe-korafe.
Ya kwatanta ADC da cewa kamar motar da aka dade ana tuka ta ce, yau shaf zai cire, gobe kuma a ce birki ya kwale da kansa.
Wadannan kalaman na Sanata Shehu Sani na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ADC ke fuskantar rarrabuwar kai tsakanin sassa daban-daban na masu ikirarin shugabancin jam’iyya.
