Mataimaki na Musamman ga tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan Kafafen Sadarwa na Zamani, Bashir Ahmad, ya nuna bacin ransa game da yadda ake alakanta jam’iyyarsu ta APC mai mulki da rikicin cikin gida na jam’iyyar ADC.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Bashir ya ce ba ya jin dadin yadda duk wani rudani da ya taso daga Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ake dora wa jam’iyyar APC alhaki, tare da zargin cewa ita ce take rura wutar rikicin.
Babban abin da ya fi daukar hankali a kalamansa shi ne yadda ya yi fatali da ikirarin shugabancin bangaren Nafiu Bala Gombe a jam’iyyar ta ADC a matsayin haramtacce.
“A gaskiya, ko a matsayina na dan APC, na san cewa Nafiu Bala Gombe ba shi ne yake wakiltar sahihin shugabancin jam’iyyar hamayya ta ADC ba.”
Bashir Ahmad ya ci gaba da kokawa kan kura-kurai da ya ce INEC na tafkawa a kan rikicin ADC, wanda hakan ke shafar ƙimar jam’iyyar APC.
Ya ce ana zargin APC da hannu a rikicin ba tare da kwararan hujjoji ba.
Ya nuna cewa INEC a matsayinta na mai zaman kanta, ya kamata ta magance wadannan matsalolin yadda ya kamata don kauce wa jita-jita.
Ya bukaci a fada wa juna gaskiya domin tabbatar da dorewar dimokradiyya.
Wannan ikirari na Bashir Ahmad ya janyo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke ganin cewa hakan wata hanya ce ta wanke jam’iyyar APC daga zargin da ake mata na kokarin dakushe jam’iyyun hamayya.
