Biyo bayan wasu wasiƙu masu cin karo da juna da ta samu daga lauyoyin ɓangarorin da ke rikici da juna, hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta tsinci kanta a tsakiyar takaddamar shari’a dangane da shugabancin jam’iyyar ADC.
A wata sanarwar manema labarai da hukumar ta fitar, ta tabbatar da karɓar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na ranar 12 ga Maris, 2026.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da Senator David Mark ya shigar, inda ta ba da umarnin a kiyaye martabar shari’ar da ke gaban babbar kotun tarayya.
Lauyoyin Hon. Nafiu Bala Gombe sun rubuta wa INEC wasiƙa suna neman lallai hukumar ta daina amincewa da David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar, sannan ta cire sunansa daga rumbun bayanan hukumar na intanet.
A sa’ilin da labarai ke yawo a kafafen sadarwa cewa tuni INEC ta aiwatar da umarnin kotun ta hanyar goge sunan Senator David Mark daga shafinta, binciken Blueprint Hausa Radio ya nuna cewa wannan bayani ba gaskiya ba ne.
Har zuwa lokacin wallafa wannan labari, sunan Senator David Mark yana nan daram a matsayin, sannan Ogbeni Rauf Aregbesola yana nan a matsayin sakataren jam’iyyar a shafin hukumar INEC.
Ko da yake akwai umarnin kotu, hukumar INEC na nazarin matakai na shari’a kafin sauya bayanan shugabannin jam’iyyu a hukumance don kaucewa saɓa wa wasu ƙa’idojin.
A daya ɓangaren, ɓangaren Hon. Nafiu Bala Gombe sun bayyana bacin ransu, inda suke zargin INEC da nuna son kai. Sun yi zargin cewa INEC ta gayyaci ɓangaren David Mark zuwa taron jam’iyyun siyasa da aka yi a ranar 24 ga Maris, tare da sa ido kan taron majalisar zartarwa NEC na ɓangaren Mark da aka yi ranar 25 ga Maris, abin da suka ce ya saɓa wa umarnin kotu.
A halin yanzu, dambarwar tana ci gaba da jan hankali yayin da ake jiran mataki na gaba da hukumar INEC za ta ɗauka bayan kammala tuntuɓar lauyoyinta.
Ku ci gaba da kasancewa da Blueprint Hausa Radio don samun sahihan labarai a kowane lokaci.
